Ku rage farashin raguna musulmai su iya yin laiya – Rokon fasto Yohanna ga masu siyar da raguna

0

Kungiyar malaman addinin musulunci da na kiristoci a Kaduna sun yi kira ga masu saida raguna su rage farashin kudin rago saboda musulmai su samiu su iya yin Laiya a wannan lokaci da Eid-El-Kabir ya karato.

Shugaban kungiyar Fasto Yohanna Buru ne ya yi wannan kira a lokacin da mambobin kungiyar ta yi tattaki zuwa kasuwannin da ake siyar da ragunaa garin Kaduna ranar Juma’a.

Yohanna ya ce kungiyar ta yi wannan ziyara ne domin ta gana da masu saida ragunan sannan a roke su su sassauta su rage kudin raguna domin talakwa ma su iya siyan ragon layya.

Ya ce yin wannan kira ya zama dole ganin yadda mutane da dama basu iya siyan ragon saboda tsadan da suka yi a bana.

Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar masu siyar da raguna Alhaji Musa Usman ya ce farashin rago ya kara kudi saboda rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan.

Ya ce a dalilin rashin tsaro kungiyar su na fama da matsalar karancin raguna musamman yanzu da ake gab da babban sallar.

A dalilin Karin farashin kudin rago mutane da dama ba za su iya yin layya ba.

A yanzu haka ragon da aka siyar a watan jiha akan farashin Naira 40,000 ya koma naira 60,000.

Share.

game da Author