KORONA: Dalilin da ya sa har yanzu ba mu amince da maganin Korona na gargajiya ba – NAFDAC

0

Hukumar kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta yi karin haske kan dalilin da ya sa har yanzu bata amince da maganin gargajiya da aka hada domin warkar da cutar korona a kasar nan ba.

Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ya ce har yanzu babu wani maganin warkar da cutar da aka hada a duniya.

Ta ce magungunan da ake da su yanzu magunguna ne da aka hada domin rage raɗaɗin cutar a jiki ba wai ya warkar da ita

Daga nan kuma sai Mojisola ta gargaɗi mutane da su rage yawan amfani da tafarnuwa da albasa wai don warkar da Korona ko yin rigakafin ta.

“Yawan cin albasa da tafarnuwa na sa warin baki da warin jiki kuma ba lalle ba ne su kare mutum daga kamuwa da korona.

“Albasa da tafarnuwa na taimakawa wajen inganta garkuwar jikin mutum amma ba su da ingancin samar wa mutum kariya daga kamuwa daga korona.

Ta ce duk wani maganin gargajiya da aka hada domin warkar da korona ba tare da hukumar NAFDAC ta tabbatar da ingancin sa ba ba magani bane.

Sannan yin amfani da maganin gargajiyan da aka hada domin warkar da korona ba tare da an nemi izinin hukumar ba ya karya dokar da hukumar ta saka na kula da ingancin magunguna da abinci a kasar nan.

Mojisola ta yi kira ga mutane da su guji yin amfani da maganin da aka hada ba tare da hukumar NAFDAC ta tabbatar da ingancin sa ba.

Idan ba a manta ba a bara PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa NAFDAC na yin gwajin magungunan warkar da Korona har guda 40 da masu hada magungunan gargajiya suka mika mata.

Share.

game da Author