‘Yan bindiga sun kama mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jiha

0

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jihar Bayelsa.

An arce da gyatumar mai shekaru 80 a duniya, mai suna Betinah Benson, a ranar Talata da dare, bayan an yi mata takakkiya a gidan ta da ke kan titin Azikoro, cikin tsoffin rukunin gidajen ‘yan majalisa da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Wannan ne karo na biyu da aka sace gyatumar aka yi garkuwa da ita.

An taɓa yin garkuwa da ita cikin 2013, shekaru takwas da su ka gabata. Sai dai kuma ‘yan sanda sun ceto ta, bayan ta shafe kwanaki bakwai a tsare.

Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Beyelsa, Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Bayelsa, Mike Okoli da kan sa ya ja tawagar jami’an bincike har zuwa gidan matar.

Ya ƙara da cewa tuni har an baza zaratan jami’an tsaron da su ka bazama domin tabbatar da sun ceto ta, an amida ta gida a cikin ƙoshin lafiya.

Share.

game da Author