‘Yan sanda sun damke wadanda suka yi wa barawo dukan tsiya ya mutu

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa wasu mutane sun lakada wa wani barawo duka inda hakan ya yayi ajalinsa.

Kakakin rundunar Shiisu Adam ya sanar da haka ranar Alhamis.

Adam ya ce sunan barawon Hassan Sale mai shekaru 40 sannan an kama shi yayin da yake kokarin shiga shagon wani mutum mai suna Garba Sama’ila.

“A ranar 13 ga Yuni da misalin karfe 10:30 Sama’ila ya kama Sale yana kokarin yi masa sata a shago. Sai ya kwara ihu jama’a suka ko rufa shi da dukan tsiya har ya ce ga duniyar ku nan.

Sale mazaunin kauyen Kyaurawa sannan ya taso daga nan ya je kauyen Chandan dake karamar hukumar Birnin Kudu domin yayi sata.

Adam ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano mutanen da suka kashe Sale wajen duka.

Share.

game da Author