Rashin kula da mata ta bata bani ya sa nake fama da tsananin talauci da neman mata, daga baya kuma na kashe ta – In ji wani Fasto

0

Wani faston cocin ‘Word Global Ministries’ dake kauyen Ikot Ataku a karamar hukumar Eket jihar Akwa-ibom Chris Enoch ya bayyana wa rundunar ‘yan sandar jihar dalilin da ya sa ya kashe matarsa.

Enoch mai shekaru 49 a duniya dake da cocin sa a cikin gidansa inda yake zama da matarsa Patience, mai shekaru 40 da ‘ya’yan su biyar, yana da dan mai shekaru 15.

Enoch ya ce ya kashe matarsa da dukan tsiya saboda itace ta sa yake fama da talauci da tsananin neman mata a waje da yake yi.

Ya ce ya kashe matarsa a lokacin da suka kicime da cacan baki shi kuma a cikin fushi ya hau ta da duka har sai da yaji bata numfashi.

Daga nan ne bayan ya tabbatar ta mutu sai ya haka Rami a bayan gidan ya birne ta.

Enoch ya aikata haka ne ranar 9 ga Yuni.

Kakakin rundunar Odiko MacDon ya yi kira ga ma’aikata da su rika hakuri da junan su suna sasanta kansu a duk lokacin da suka yi fushi da juna a gida.

MacDon ya ce rundunar ba za ta yi kasa-kasa ba wajen kamo mazajen dake cin zarafin matansu a jihar.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda matasan Okon suka hako gawar matar fasto Enoch a cikin gidan su inda ya binne ta.

Shugaban matasan Okon Effiong Johnson ya ce sun samu labarin cewa ‘ya’yan Enoch sun shiga gidajen makwabta suna cigiyan mahaifiyar su da suka yi kwanaki hudu basu saka ta a ido ba.

Johnson ya ce yin haka ya sa suka shiga gidan Enoch yin bincike inda suka gano gawar matar a cikin wani rami mara zurfi.

Sai dai ‘ya’yan Enoch sun bayyana wa ‘yan sanda cewa ba tun yanzu mahaifin su ya kan yi barazanar kashe mahaifiyarsu.

Share.

game da Author