Yadda tsohon dan majalisa ya yada bayanan karya kan allurar rigakafin COVID-19 ya kuma yaudari ma’abota shafukan shi na yanar gizo -Binciken DUBAWA

0

Ga mutane da yawa, Dino Melaye mutun ne mai baiwa iri-iri- shi dan siyasa ne, wanda ba ya fargaban fadin albarkacin bakinsa, ya yi fafutuka a shekarun farko kuma ya rubuta littafi. Baya ga siyasa, wasu fannonin kwarewar tsohon sanatan sun hada da wakoki, da rawa, wadanda ya ke yawan amfani da su a duk sadda ya fiskanci rikicin siyasa wadanda kuma suke jan hankalin ‘yan Najeriya zuwa gare shi.

A daya daga cikin wakokin shi, wadda ya sami karbuwa sosai wajen jama’a, wadda kuma aka fi sani da “ajekun iya”. An ga Mr. Melaye yana waka yana rawa bayan da wani kwamitin majalisar dattijai ta wanke shi daga zargin amfani da takardun kammala makaranta na bogi. A wasu wakokin kuma ya kan yi na da abokan hammaya, sai kuma wasu lokutan wakokin yabo ne ga Ubangiji musamman a lokutan da ya yi nasara.

Yayinda baiwar tasa da aikin siyasar a ko yaushe ke tattare da rigingimu, tsohon dan majalisar wanda ya wakilci mazabar sa a majalisar wakilai da na dattijai ya na yawan ma’amala da ma’abota shafukan shi na yanar gizo musamman a Tiwita.

Wannan ma’amalar ta dauki sabon salo a shekarar 2020 sadda Mr Melaye ya fara sharhi a kan COVID-19. Daga karshen shekara ta 2020 ya yi tsokaci sosai a shafin twitter dangane da allurar rigakafin coronavirus wadanda yawancinsu suka kasance karya.

Wajen yin amfani da abubuwan binciken da tiwitar ta tanadar, mun fara binciken da amfani da kalmomin ‘COVID-19’ da ‘Vaccine’. Sakamakon nan da nan ya fitar da sharhuna fiye da dozin wadanda ake dangantawa da Mr Melaye, wadanda kuma ake zargi suna dauke da batutuwa marasa gaskiya dangane da allurar rigakafin COVID-19.

Da muka tantance yawan masu amfani da sharhin da ma tasirin da yake da shi, mun gano cewa milliyoyin mutane ne suka karanta sharhin a yayinda wasu dubbai kuma suka turawa abokansu. Dan haka ne ma duk da cewa babu kwakwarar hujja muna iya cewa maganganun shi na tasiri sosai. Ko daga farkon bullar cutar, Mr. Melaye yana da ma’abota sama da milliyan biyu a shafin Tiwita kuma ga wadansu ma’abotan na sa, bayanan shi ne wuka su ne nama. ‘Yan Najeriya kalilan ne suke da ma’abotan da suka fi na shi yawa.

Taskar mai bin diddigin gaskiya

Ranar 31 ga watan Disemba Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta amince da allurar rigakafin Pfizer/BioNTech dan amfani da shi a matakin gaggawa wajen kawar da kwayar cutar. Makonni biyu kafin nan, Mr Melaye ya yi bidiyo a Tiwita inda ya ke baiwa ma’abota shafin na sa shawara kan allurar rigakafin. Da aka yi amfani da manhajan binciken duk wani bayanin da aka taba sanyawa a yanar gizo mai suna Wayback Machine, sadda ya zo shekarar 2020 sai ya fara tantancewa a hankali saboda yawan bayanai. (December 16 2020) Mr. Melaye na da mutane miliyan 2.55 da ke bin shi a shafin.

Bidiyon wanda tsohon dan majalisar ya yi wa taken “Say no to COVID 19 Vaccine” wato ku guji allurar rigakafin COVID-19 na da tsawon minti daya da sakan 50. Ya fara da yin kira ga ‘yan Afirka musamman ‘yan Najeriya da su guji yin amfani da kowane irin allurar rigakafi, in dai ta COVID-19 ce.

Ya kara da cewa, “Na tsawon shekaru 100 yanzu mun kasa gano allurar rigakafin cutar daji/Cancer, na tsawon shekaru 40 yanzu ba mu sami allurar rigakafin cutar SIDA/cuta mai karya garkuwar jiki ba. An sake shafe wasu shekaru 100n kuma ana neman allurar rigakafin cutar suga/Diabetes. Yaya za’a ce a cikin shekara guda kadai har an gano allurar rigakafin COVID-19?

“Ina kira ga shuwagabannin Afirka, ka da su yarda kasashen yamma su yi gwaje-gwajen su bisa dalilai na shaidanci da al’ummar Afirka”

“Bamu yarda da amfani da wata allurar rigakafi a Afirka ba. Muna kira ga ministan lafiya ta tarayyar Najeria da ya daina ma’amala da wadanda ke neman bamu alluran”

Ba tare da wata kwakwarar hujja ba, Mr Melaye ya ce “bayanan sirri” sun nuna cewa mutanen da suka karbi allurar sun mutu bayan kwanaki uku.

Ya zuwa ranar Juma’a hudu ga watan Yuni, bayanan Tiwita sun nuna cewa jama’a sun kalli bidiyon har sau dubu 75 kuma mutane sama da dubu uku sun nuna amincewarsu da kalaman shi a yayin da wasu 1,800 suka turawa abokai bidiyon.

Wannan bidiyon bai tsaya a shafin Melaye kadai ba. Mutane sun yada bidiyon fiye da lokuta 2000. Tiwita ta nuna cewa akwai mutane biyar masu ma’abota da yawa a shafin wadanda su ma sun sanya bidiyon a shafukansu kuma ya dauki hankalin jama’a yadda ba’a zato.

Da ma’abota fiye da dubu 100 FS Yusuf S Yusuf (@_Yusuf, Dr. Ben Gbenro (@bengbenro), Bruce Batemen Esq (@demigodgeous), Nwankpa (@Nwankpa_A) and Daddy G.O (oboy_jay) duk sun yada bidiyon a shafukansu.

An kuma sanya bidiyon a shafin bidiyoyi na YouTube. Manyan shafuka biyar da suka sanya bidiyon a manhajar YouTube sun ja hankali sosai inda aka kalli bidiyon fiye da lokuta dubu 700. Sauran taskoki da shafukan yanar gizo ma sun dauki labarin da bidiyon Mr. Melaye.

Yawancin wadanda suka yi tsokaci dangane da batun a karkashin wannan bidiyo sun nuna rashin yarda, akwai ma wadanda suka wallafa hujjojin da suka karyata wannan zargi. Sai dai hujjojin sun zo a makare, bayan dimbin jama’a sun riga sun yi ma’amala da sakon.

A yayinda wasu suka sha alwashin cewa ba zasu karbi allurar ba, wasu sun shawarci jama’a da su dauki kalaman dan siyasar da gaske tunda ruwa ba ya tsami banza.

“Abun mamaki ne yadda wadansu suke watsi da sako mai mahimmanci kamar wannan a shafin nan. Kamata ya yi a kara fadada sakon,” wani mai amfani da shafin ya bayyana.

Akwai wadanda suka ga sakon amma ba su yi ma’amala da shi ba, sai dai hakan ba wai dan labarin allurar rigakafi ba ne. Zamu duba dalilan da ya janyo haka daga baya a cikin wannan binciken, yanzu bari mu fara da sauran zarge-zarge marasa tushe na Mr. Melaye dangane da rashin ingancin allurar rigakafin COVID-19.

A farkon shekarar 2021, wani hoton Remdesivir, daya daga cikin magungunan da ake amfani da su a cututtuka irinsu Hepatitis ko kuma kumburin hanta, da kwayar cutar Ebola, ta bayyana a shafukan sada zumunta. A kan kwalin maganin an rubuta cewa wannan magani dan amfanin kasashe 47 a nahiyar Afirka ne, bai dace a sayar da shi a kasashen Amirka, Canada da Tarayyar Turai (EU) ba.

Mr Melaye sai ya dauki wannan hoto ya wallafa a shafin shi yana tambaya a fayyace ma sa abin da hakan ke nufi “what is the meaning of this biko?” Duk da yunkurin da aka yi a karyata, da yawa da ke bin shafin shi a Tiwita sun amince da zargin da ya yi. Akalla mutane dubu guda suka nuna alamar amincewa da zargin a shafuka daban-daban.

“Ya Allah! suna neman kashe mu ne tunda COVID-19 bai yi ba”, a cewar wani. Wani kuma cewa ya yi “Wa kuma ya kula cewa an zame kasashen su Aljeriya da Masar da Moroko da Tunisiya da Libiya? Sudan ce kasar da aka sanya daga kasashen da ke yankin arewacin Afirka. Wata kila hankalinsu na kan bakaken fata ne kadai.”

Binciken kwa-kwaf kan martanonin da aka mayar sun nuna cewa fiye da rabi (rabin sharhohi 538 – daga 6 ga watan Yuni 2021) sun yarda da wannan magana. Sharhin ya kuma jaddada makircin da ake zargin turawa da kullawa na shafe kasashen Afirka daga doron kasa. Sai dai duk da haka Mr. Melaye bai gama ba.

Ranar 21 ga watan Janairu, ya sake wallafa wani bidiyo mai tsawon minti 2 yana yi da gwamnatin tarayya dangane da allurar rigakafi, yana cewa ya kamata a kirkiro kowace allura ta yadda za ta dace da irin nau’in COVID-19 din da ake samu a kasar.

Bayan wata biyu sai ya sake zuwa ya fara kushe allurar rigakafin AstraZeneca wanda gwamnatin tarayya ta samu. A wata hira da ya yi da gidan talbijin na Roots TV, wadanda mutane dubbai ke zuwa shafinsu. Mr. Melaye ya yi zargin cewa AstraZeneca shi ne mara karfi a cikin duk wadanda alluran da aka kirkiro. A wannan lokacin sai kuma ya yi kamar ya sauya matsayin shi ne dangane da allurar rigakafin, domin a maimakon cewa kada a karba yadda ya saba sai ya fara cewa a yi hattara wajen zaben allurar.

“Ba wai ina nufin Najeriya ta guji karbar allurar rigakafin COVID-19 ba ne, abun da nake nufi shi ne akwai allurai hudu da Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da su – AstraZeneca, Johnson & Johnson, Pfizer-BioNTech COVID-19 da kuma Moderna. A cikin su, AstraZeneca ce mara karfi kuma ita ce ta fi hadari.”

Daga baya sai ya sake sanya wani hoto a twitter inda ya ke kwatanta duk alluran rigakafin yana kushe su. Dan haka ne ma DUBAWA ta gudanar da binciken da ya karyata duk wadannan zarge-zargen. Za’a iya samun binciken a shafukanmu.

Bacin hakan, yawancin wadanda suka karanta sun nuna amincewarsu. To amma me ya faru a zahiri bayan sun karanta sun bar dandalin yanar gizo?

Abubuwan da ke tabbatar da son zuciya

A watan Janairun 2021, wata rana lokacin wa’azi a daya daga cikin cocunan Redeemed wanda ya yi suna a babban birnin Tarayya (FCT) Abuja. Wani daga cikin manyan faston cocin, wanda za mu sakaya sunansa bisa dalilai na kariya, ya yanke shawarar yin wa’azi kan tashin kiyama.

“Faston ya ce mana ba wai yana so ya hana mu bane amma ba zai ba mu shawarar karbar allurar rigakafin ba. Ya ce mana kan shi ba zai karbi allurar ba. A gani na ya hana mu karba ne kawai a fakaice, ba tare da ya fito fili a fadi hakan karara ba,” a cewar Milon, daya daga cikin mambobin cocin.

A wannan lokacin ba’a riga an kawo allurar rigakafin ba amma ana sa ran kawo wa daga COVAX ba da dadewa ba. Ranar 2 ga watan Maris, aka shigo da milliyan 4 na allurar rigakafin kuma cikin makonni kadan aka fara yi ma mutane allurar a Najeriya.

Bacin matsayin da mambobin coci da shugabananninsu suka dauka, wata ma’aikaciyar gwamnati mai zuwa cocin ta yi gaban kanta ta karbi allurar rigakafin a farkon watan Afrilu sai dai bayan mako guda da yin hakan ta rasu.

“Mutane da yawa sun sha alwashin cewa allurar ce ta kashe shi. Har ma aka rika amfani da sharhin Dino Melaye a matsayin hujja duk sadda masu zuwa cocin suke tsokaci dangane da allurar.

“Bayan rasuwarta sai ka ji ana cewa an ba mu shawarar kada mu karba amma ta je ta yi gaban kanta. Babu shakka mutuwarta ya karfafa tasirin kalamansa. Ba na ji ko kashi daya cikin dari na masu zuwa cocin sun karbi allurar rigakafin,” a cewar Milon.

“Musamman matasan cocinmu, su sun yadda cewa tunda Dino Melaye ya taba kasasncewa a jam’iyya mai mulki ta APC tabbas akwai kanshin gaskiya a batun tunda ruwa ba ya tsami banza. ‘yar uwata ba zata yi allurar ba, kuma na tabbata saboda irin sharhin da Melaye ke yi ne domin ta na bin shafinshi a tiwita kuma tana son shi sosai,” in ji Milon.

A watan Maris, Milon ya karbi kashin farko na allurar, yana sa ran samun kashi na biyu nan ba da dadewa ba amma ko daya ba zai fadawa ‘yan uwanshi ko mambobin cocin shi ba.

Duk da cewa mutun ne kadai zai yanke wa kansa shawarar yin allurar rigakafi, bai kamata a yi watsi da irin tasirin da kalaman manyan mutanen da ake girmamawa a al’umma, irin su Deno Melaye ke da shi a kan mutane ba. Mun sami tabbacin haka ne daga hirrarrakin da muka yi da wasu daga cikin matasan cocin.

“Yadda wasu manyan mutane a kasar irin su Dino Melaye da Pasto Chris ke nuna adawa da allurar rigakafin ya isa ya hana mutane karba (allurar rigakafin),” wata mai zuwa cocin ta bayyana, tana kuma karawa da cewa “Yadda kasar ta ke yanzu, yana da wuya mutun ya yarda da jami’an gwamnati, sai ka rika ji kaman kai fa ba ka da yadda za ka tabbatar cewa ba wata makarkashiya ce ake sakayawa da batun allurar ba.”

Melaye bai amsa gayyatar hirar da muka tura mi shi a sakon Whatsapp ba, bayan da muka ga cewa duk wayoyin shi a rufe suke.

Bari mu koma coci, wasu karin matasa biyar wadanda suka yi magana sun ce ba zasu karbi allurar ba. Shugabanin addini sun riga sun gargade su kuma shugabanin siyasarsu ma ba’a shirye suke su yi karba ba. Dan haka me za sa su su karba?

Share.

game da Author