Za ayi zaben kujerar dan majalisar jiha na karamar hukumar Sabon Garin Zaria, ranar 19 ga Yuni – INEC

0

Hukumar Zabe mai zaman kanta za ta gudanar da zaben cike gurbi na mazabar Sabon garin Zaria ranar 19 ga Yuni.

Idan ba a manta ba majalisar jihar Kaduna ta bayyana kujerar tsohon shugaban majalisar jihar Aminu Shagali a matsayin wanda babu wani a akai.

Majalisar ta ce Shagali ya yi kwanaki 360 bai halarci zaman majalisar ba da hakan ya saba dokar majalisar.

A dalilin haka yasa majalisar ta bayyana kujerar sa a matsayin babu kowa a kai.

Hukumar INEC ta ce za a gudanar zaben a gundumomi 8 da suka hada da Chika, Muchia, Jushin Waje, Hanwa, Dogarawa, Unguwan Gabas da Zabi.

Jam’iyyun APC, PDP, PRP duk sun mika ‘Yan takara a zaben.

Share.

game da Author