UMARNIN BUHARI: Na kara nanatawa, duk wanda aka gani da AK-47 ku bindige shi

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nanata umarnin da ys taba bai wa jami’an tsaro cewa duk wanda su ka gani da bindiga kirar AK-47, to a bindige shi.

Buhari ya nanata wannan umarni kuma gargadi a ranar Alhamis a Lagos, lokacin da ya kai ziyarar bude wasu ayyukan Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Lagos.

Buhari ya taba bada irin wannan umarni cewa matsawar mutum ba jami’in tsaro ba ne, to da an gan shi rike da AK-47, to a sheka shi lahira kawai.

“Gwamnati na za ta kara tashi tsaye wajen dandana wa duk wani mai banka wa Ofisoshin ‘Yan Sanda wuta, irin kudar laifin da ya ke aikatawa.”

Buhari ya yi wannan jawabi wurin bukin damka wa ‘Yan Sandan Jihar Lagos kayan aiki da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi.

Buhari ya yi gargadin cewa duk kasar da al’ummar ta ta maida ‘yan sandan kasar da kadarorin gwamnati abin kai wa hare-hare, to tabbas ta kamo hanyar tarwatsewa.” Inji Buhari.

“A matsayi na na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, babban nauyin da ke kai na shi ne na kare rayuka da dukiyoyin jama’a. To duk da irin kalubalen da kasar nan ke fuskanta, ina tabbatar maku cewa za mu tsare kasar nan mu kawo tsaro.”

Share.

game da Author