LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda Minista Isa Pantami ya ziyarci Sheikh Dahiru Bauchi a Bauchi

0

A ranar Juma’ar nan ce Sheikh Dahiru Bauchi ya karbi bakuncin Ministan Sadarwa, Isa Pantami.

Pantami wanda babban Sheikh ne na Sakafiyya, ya ziyarci babban Sheikh na Dariƙar Tijjaniyya a gidan sa da ke Bauchi.

Da ya ke bayanin karɓar Pantami, Dahiru Bauchi ya jinjina masa kan irin ayyukan da ya ke yi.

Daga nan kuma ya bayyana Pantami a matsayin Minista mahardacin Alƙur’ani na farko a tarihin Najeriya.

Wannan ziyara dai ta burge bangaren Tijjaniyya da su ma ‘yan Sakafiyya, ganin yadda bangarorin kowane fahimtar sa da akidar sa a sha’anin addinin Musulunci sun bambanta da juna.

Share.

game da Author