Ƙungiyar masu yin gurasa ta jihar Kano sun bayyan cewa lallai za su fara yajin aikin gama gari idan har farashin fulawa bai yi kasa ba.
Shugaban kungiyar Fatima Auwalu ta sanar da haka ranar Laraba a garin Kano.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata kungiyar ta yi yajin aiki na yin gargaɗi saboda tsananin tsadar fulawa a jihar.
Fatima ta ce duk da sun dakatar da yajin aikin farashin fulawa bai yi kasa ba.
Ta ce kafin fulawar ya kara kuɗi suka siye shi Naira 9,500 amma yanzu ya tashi zuwa Naira 16,200.
“Sannan fulawar da ake saidawa da tsada yanzu ba shi da amincin na da.
Fatima ta ce kungiyar ta janye yajin aikin ne a dalilin rokon da Kwamishinan ƴan sanda da ƙungiyoyin suka yi mata.
Ta yi kira ga masu yin fulawa da wadanda ke siyar da ita da su tausaya wa masu yin gurasa su rage kuɗin fulawar a jihar.
Gurasa na daga cikin abinci mai arha da talaka ke samu ya saka a bakin salati, kuma ya daɗe bai nemi abinci ba saidai yayi ta kwankwaɗan ruwa kawai.
Da ₦50 ɗin ka zuwa 100 sai yi nak, sannan ka ka kama bakin ka kayi shiru kamar ka yi asiwaki da cinyoyin kaji, amma kuma tsadar fulawa na neman ya kai talaka ya baro, domin gurasa zai gagareshi.