‘Yan bindiga sun sace magidanta biyu a Abuja, sun saka miliyan 10 kudin fansa akan kowannen su

0

‘Yan bindiga sun sace wasu magidanta biyu a unguwar Kubwa dake babban birnin Tarayya, Abuja, inda suka sace wasu magidanta biyu cikin dare ranar Juma’a.

Kamar yadda mai dakin daya daga cikin wadanda aka sace Victoria Somorife ta bayyana cewa maharan sun afka musu a lokacin da suke barci a gida da dare.

” Maharan sun yi ta buga kofar shiga gidan mu sai muka tattara kan mu tara da yara muka kule cikin baya muka kulle. Suna shiga cikin gidan bayan balla kofar da suka yi sai sai suka nufo kai tsaye zuwa bayin.

“Da suka balle kofar sai suka fara jibgar maigida na. Babu inda ba su shiga ba a gidan suka kwashe mana wayoyi, komfutocin mu, kayan sawa, abinci, takalma da duk wani abin amfani. Daga nan sai suka ce wa maigida na ya saka takalmin sa ya fito su tafi, sun sace shi.

Da suka fita daga gidan mu sai suka ci gaba da harbin bindiga a sama sannan suka afka gidan makwabcin mu.

Matar mutum na biyu da ‘yan bindigan suka sace Oyinlola Josiah tace ” ko da maharan suka karya kofar shiga gidan suka afko ciki, ba su iske kowa a ba sai maigidana, domin ya ce mu shige can cikin kurdin bayan gida mu labe mu yi shiri. Kuma Ikon Allah ba mu ma rufa kofar ba.

” Maigida na ne su ka rika jibga suna ce masa ina ya’yanka? Haka nan dai suka ci gaba sauran abokan aikin su kuma suna ta kwasar duk wani abu da suka gani, wayouin mu ne, komfuta, kayan sawa, harda abinci ma sun diba.

Rundunar ‘Yan sandan Abuja ta ce ta aika jami’an tsaro su bi sawun wadannan ‘yan bindiga.

Yan bindigan sun bukaci a biya naira miliyan 10 kowannen su kafin su sake ko su aika su barzahu.

Share.

game da Author