Mira Mehra, sunan wata mata ce mai ƙwazon noma. Idan ba ka taba jin sunan ta ba, to yau ga labarin matar da ta baro harkokin da ta ke yi a Amurka, ta kafa masana’antar sarrafa tumatir da naira biliyan 4, a Jihar Kaduna.
Sunan masana’antar ta Tomato-Jos, wadda ake sarrafa tumatir a Kaduna. Mira ta ce an kafa masana’antar tun cikin 2014.
Ta zabi Kaduna a matsayin inda ta kafa masana’antar, saboda a cewar ta kasar wajen ta fi dacewa da irin tumatir din da su ke nomawa kuma su ke sarrafawa.
“Sannan kuma mun sa sunan Jos ne saboda akwai wani samfurin tumarir mai tsada a Jos, wanda jama’a da dama ke dububin sa. To na mu irin sa ne. Saboda na mu ba irin wanda ake wa rubutun Chana ba ne.
“Kuma ka san na taba yin zama a Najeriya tsakanin 2008 zuwa 2012. To abin da ya ba ni sha’awar kafa masana’antar nan a karkara, na yi aikin kula da kiwon lafiya a yankunan karkara a Najeriya. Na ga irin yadda talauci ya yi masu katutu. Sai na yanke shawarar dawowa cikin su domin na taimaka wa bunkasa rayuwar su.
“Wato na rika cin karo da irin gaganiyar da mutanen karkara ke yi wajen ganin su na fadi-tashin ganin irin wahalhalun su. Sai na ce bari dai na shiga cikin su na inganta rayuwar su, watakila ni ma na samu riba a lamarin.”
“Masana’antar mu zuwa yanzu an danƙara mata jari ya kai na dala miliyan 10, kwatankwacin naira biliyan 4 kenan. Amma ka san irin wannan makudan kudade masu yawa na tafiya ne wajen gina masana’antar da kuma musamman wajen zuba kayan aiki.
“Kafa masana’anta ba abu ne mai sauki ba. Ka ga har yanzu ana ta gaganiya ce, daga wannan sai wannan. Ribar kirki ma ba a fara samu ba. To amma wadanda su ka zuba jarin su a masana’antar, mutane ne masu hakuri kwarai da juriya. Sun san nan gaba za a amfana saosai.”
Da ta koma batun tumatir din kuma, ta ce gonar noman tumatir din ta kai fadin hekta 500. Ta na da ma’aikata mutum 60 sai kuma masu aikin wucin-gadi mutum 15.
“Batun matsalar tsaro kuwa mun yi kokaarin ganin sojoji da ‘yan sanda da ‘yan bijilante da al’ummar gari sun san da mu. Su na ba mu hadin kai.
“Inda mu ke da matsala har yanzu, shi ne batun rashin titi mai kyau da matsalar wutar lantarki da kuma wani lokaci matsalar intanet.”
Da aka tambaye ta batun takin zamani. Ta ce sun daina saye a wajen kananan ‘yan kasuwa, sun koma saye a hannun manyan dillalai.
“A Amurka taki ba wata tsiya ba ce, kuma ga shi nan a wadace. Amma da na dawo nan, sai na ga taki ya zama sai su wane da wane.” Inji ta.