Mutuwar su Janar Attahiru ta kara dagula matsalolin tsaron kasar nan – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mutuwar Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da sauran manyan hafsoshin sojoji 10, ta kara dagula matsalar tsaron Najeria.

Buhari ya bayyana haka lokacin da Sbugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar manyan sojojin.

Fayemi ya kai ta’aziyyar ce tare da rakiyar Shugaban Riko na Jam’iyyar APC, kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala-Buni da kuma Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi.

Buhari ya ce ko shakka babu mutuwar su Attahiru ta kara dagula matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan.

Tare da kara shan alwashin dakile matsalolin tsaro, Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a.

” Mutuwar su wa’adi ne da ya cika, wanda babu wanda ya san lokacin cikar sa sai Allah. Sun mutu a daidai lokacin da kasar nan ke fuskantar matsanancin kalubale.

” Rasa wadannan hazikai kuma jajirtattun sojoji babbar matsala ce ga tsaron kasar nan. Amma dai za mu ci gaba da aiki tukuru, tare kuma da kari da yin addu’o’i domin shawo kan lamarin.

Fayemi ya ce tabbas sun san mutuwar hazikan sojojin ta taba Shugaba Buhari da kuma Gwamnatin sa.

” Lokacin ka amince da kiraye kirayen jama’a har ka amince za ka canja su, mun hakkake cewa za ka yi sabbin zubin wadansu hazikan da su ka dace. Ka yi hakan kuma an gani an shaida. Har an fara ganin irin kokarin da su ke yi.”

Fayemi ya ce rashin su Attahiru babban rashi ne sosai. Shi ma ya yi masu addu’ar samun rahama, kuma ya yi wa Buhari da iyalan mamatan ta’aziyya.

Share.

game da Author