A ranar Laraba ne aka buka wasan karshe na cin Kofin Europa tsakanin kungiyoyin Manchester United na kasar Ingila da Villareal na Kasar Spain.
Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci aka jefa wa Manchester Kwallo a ragar ta, ba dade ba ana fafatawa, mowa na kai hara sai Manchester united ta rama kwallon, ya zama daya da daya, 1-1.
Babu wanda ya sake yarda kwallo ta shiga ragar aka yi ta fama har dai lokaci ya cika aka.
Bayan haka sai aka kara musu rabin awa su ci gaba da fafatwa har sai an samu wanda yayi nasara.
Nan ma haka aka yi da doka kwallo babu wanda ya iya cin wani har minti 30 din ya cika.
Daga nan kuma sai dukan daga kai sai gola.
Sai da yan kwallon kungiyoyin biyu kaf suka buga daga kai sai mai tsaron raga, babu wanda ya bai ci ba, daga karshe sai su masu tsaron gidan suka buga.
Golin Villareal ne ya fara buga wa, ya kuma ci. Sai dai kash, da De Gea na Manchester ya buga nashi, sai golin Villareal ya buge kwallon.
An tashi wasa dai Manchester United na da kwallaye 11, ita kuma Villareal ta zura kwallaye 12 a ragar Manchester. Kwallaye 11 a bugun daga kai sai Gola, 1 kuma a lokacin wasa.