Majalisa ta yi wa Bawan EFCC tambayoyi kan hada-hadar kudade a zamanin Magu

0

An bankado wasu hada-hadar kudade a ofishin EFCC da Majalisa ke zargin an yi ba bisa ka’ida ba, a zamanin tsohon Shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

An bankado hada-hadar a lokacin da Shugaban EFCC na yanzu Abdulrasheed Bawa ya bayyana a gaban Majalisa, yayin ci gaba da binciken yadda aka yi da makudan kudaden satar da aka kwato daga hannayen barayin gwamnati.

Tun farkon jawabin sa, Bawa ya ce EFCC hukuma ce wadda ke da kasafin kudin ta na ta na kan da.

“EFCC ba ta taba karbar ko sisi daga Asusun Tara Kudaden Sata ba.”

Gama jawabin sa ke da wuya, sai Honorabul Darlington Nwakocha, ya ɗaga masa takardar shaidar a cikin 2017 tsohon Shugaban EFCC Ibrahim Magu ya kamfaci naira miliyan 3 da ɗoriya, ya biya Africa Association of African Anti-Curruption Authorities.

Bawa ya bayyana cewa lokacin da aka yi waccan hada-hadar da ake zargi ba shi ne shugaban EFCC ba.

“To ni dai ban fi kwanaki 100 da zama Shugaban EFCC ba.Ina bukatar a ba lokaci na yi bincike na gano yadda batun ya ke.

Daga nan kuma an rika bijiro wa Bawa wasu hada-hadar kudade da aka yi a baya. Su din ma dai ya ce tunda ba shi ne kan shugabanci a lokacin ba, ba zai iya cewa komai ba.

“Ni ina ganin ko da ma an debi kudin an yi wani abu da su a lokacin, to zai iya kasancewa wani abu ne ka iya tasowa a lokacin, har a bada umarnin yin haka din.

Yayin da aka ci gaba da bankaɗo wasu hada-hadar, Bawa ya nemi uzirin a bar shi ya fita, domin ya na da wani taro mai muhimmanci a kan sha’anin tsaro.

Nan take sai Shugaban Kwamitin Binciken Kudaden Sata da aka Kwato a Hannun Barayin Gwamnati, Hinorabul Adejero ya ce masa, “Ka na nufin abin da mu ke yi nan ba mai muhimmanci ba ne kenan?”

Ana sa rai a zama na gaba Bawa zai yi karin haske akan kuɗaɗen waɗanda aka rika fitarwa a lokacin Magu.

Share.

game da Author