AN DINKE BARAKA: Khalifa Sanusi ya kai ziyara Bauchi, ya gana da Sheikh Dahiru Bauchi

0

Babban malamin ɗarikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya amince da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, a matsayin Khalifan darikar a Najeriya.

Malam Dahiru ya amince da Khalifancin sarki Sanusi ne a lokacin da tsohon sarkin ya kai masa ziyara har gida a Jihar Bauchi.

Idan ba a manta ba a makon jiya ne Sheikh Inyas ya nada tsohon sarkin Kano Sanusi II khalifan darikar Tijjaniya a Najeriya bayan ya kai ziyarar ban girma kasar Senegal.

Khalifah Sanusi ya kai wa Mal Dahiru shaidar ya gani.

Yayi masa addu’a da fatan Alkhairi.

Share.

game da Author