Yadda ake haɗa abin sha mai daɗi da gamsarwa da Maltina cikin ɗan ƙankanin lokaci

0

Sanin kowa ne cewa idan nishaɗi ake bukata kuma ake so aji musamman idan a na bukatar jika makogoro a kuma gamsu, babu kamar a kwankwaɗi Maltina.

To yanzu garin daɗi ya zo kusa domin da Maltina za a iya haɗa abin sha don samu nishaɗi da kuma burge iyali da baki a koda yaushe.

Bai tsaya ga baki da iyalan gida ba, hatta yara za a iya hada musu wannan abin sha domin su sha a gida da kuma a makaranta lokacin Tara.

https://youtube.com/shorts/GYk_ESjh7go?feature=share

Yadda ake hada wannan abin sha

1 – Za a samu ‘Ice Cream’ mai dandanon Vanilla sai a dibi kamar babban cokali uku zuwa hudu a saka a cikin kofin niƙa na zamani.

2 – Daga nan sai a zuba karamin cokali na sinadarin ‘Vanilla essence’.

3 – Sai kuma a ƙara da ƙaramin cokali na sinadarin ‘Chocolate essence’

4 – Sai kuma a dildila  rabin kwalba na Maltina a cikin wannan kofin niƙa.

Bayan an yi haka sai a marƙada shi duka gaba ɗaya, wato a nike shi.

Daga nan sai shan lagwada.

Za a zuba shi ciki kofi ko kuma kwano, sannan za a iya kara masa ‘Ice cream’ mai dandanon ‘Vanilla’ a sama kafin a sha.

https://youtube.com/shorts/GYk_ESjh7go?feature=share

Share.

game da Author