YAKIN GEIDAM: Sama da mutum 2000 sun tsere daga mahaifar Sufeto Janar Alkali saboda mamayar Boko Haram

0

Sama da mutum 2000 su ka arce daga garin Geidam sanadiyyar mamayar da Boko Haram su ka yi wa cikin garin tsawon kwanaki biyu, tun daga ranar Juma’a.

Mutanen na ci gaba da arcewa saboda bata-kashin da ake tabkawa tsakanin maharan da sojojin Najeriya.

Babban Sakataren Hukumar Agajin Jihar Yobe (YOSEMA), Mohammed Goje, ya bayyana PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa wadanda su ka tsere sun samu matsuguni a sansanonin garuruwan Yusufari da Yunusari.

Ya kara da cewa hukumar sa na bibiyar mutanen da ke tserewa daga Geidam domin tabbatar da hanyar da agaji zai kai gare su.

“Daga cikin aikin YOSEMA shi ne ta tabbatar dukkan wadanda yaki ya kora daga muhallan su sun samu agajin gaggawan da ya kamata su samu.

“Tun jiya YOSEMA ta fitar da wadanda aka ji wa ciwo ta harbin bindiga, inda a yanzu ake ci gaba da kula da su a asibitocin gwamnati.

“Kuma wannan hukuma ta tantance wurare uku da wadanda su ka tsere daga Geidam su ka yi dandazo. Shi ma Gwamna Mai Mala ya isa garin Yunudari inda ya fara raba kayan agaji, musamman ganin cewa an kori mutanen a cikin watan azumin Ramadan.

YOSEMA ta buga sanarwar neman tallafi daga masu halin bayarwa a shafin hukumar na Twitter.

Wasu rahotanni sun nuna cewa har yanzu Boko Haram su na cikin garin, su na bi gida-gida su na zakulo wasu ba’arin mutane su na hukunta su.

Share.

game da Author