Wai ina wakar da Rarara ya karbi kudin talakawa ya yi barazanar zai yi wa Buhari? Daga Asabe Dattijo

0

Fitaccen mawakin APC kuma mawakin shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Abdullahi Ganduje na jihar Kano Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ya yi buris da mutane bayan ya yi barazanar cewa zai yi wa Buhari waka kuma zai lissafo ayyukan da yayi a cikin wakar fiye da 100.

Sai dai abin kamar da wuya, kila ko ya manta ne ko kuma barazana ce kawai yayi a lokacin don ya burge wasu ko kuma dai ya na so cika masa aljifai ne.

A hazakar mawaki Rarara mutane sun yi zaton kafin a gama dankara masa kudi a asusun bankin sa da ya rarraba ana loda masa kudi a ciki, za a wayi gari ne Najeriya ta dauka ana ta shagali da sauraren wakar sai aka ji shiru kusan shekara daya kenan bai ce komai a kai ba ya ja bakin sa yayi shiru, bayan ya ji miliyoyi a aljihun sa.

Haba Rarara, irin kurin da kayi, barazana da nuna ashirye kake, kamar ma wakar ka riga ka yi ta sai kuma aka ji tsit bayan kudi da ka shake ya sa dole wasu su ce wai lafiya kuwa, ko dai kuma labarin ya canja ne.

Ni ma nazari nake sai na tuna wannan waka da kace mu biya ka yi wa Buhari, mun biya kuma mun ji shiru.

Muna nan dai muna sauraren ka, amma ko dai yanzu ka saki wakar, ba haka aka so ba, domin irin kurin da kayi baya misaltuwa.

Ya ce mana akwai ayyuka da Buhari ya yi su kuma har ya kammala su 192 wabda su e zai lassafo a wakar ba a sake jin duriyarsa ba. Ko ba a gama shirya wakar ba ce kusan shekara daya da cake kudin mutane.

Share.

game da Author