Buhari ya maida wa Gwamna Ortom raddi

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya maida wa Gwamna Sanuel Ortom na Jihar Benuwai raddin zargin da ya yi masa cewa ya yi biris ‘yan bindiga na kashe al’ummar jihar Bemuwai ya ki yin komai.

Buhari ya bayyana cewa zargin da Ortom ya yi abin takaici ne matuka, kuma abun haushi da bacin rai, musamman ganin daga bakin wanda zargin ya fito.

Gwamna Ortom ya yi kakkausar su ka ga Buhari cewa ya kauda ido Fulani na kashe jama’a a jihar sa.

Ortom ya buga misali da yadda ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum 70 a Karamar Hukumar Makurdi, cikin makonni biyu.

Sannan kuma ya koka da kisan wasu mutum bakwai a cikin Sansanin Gudun Hijira da ke kauyen Abegena, a ranar Litinin.

Daga nan Ortom ya yi kira ga Buhari da ya tashi tsaye, ya farka daga barci domin ya kare ragukan al’ummar kasar nan.

“Na san matsalar tsaron da ake fama da ita ta zama ruwan dare ko ina a kasar nan. To amma a gaskiyar magana babu gwamnan da zai ji dadi ya ga a kullum ana kashe jama’ar jihar sa, kuma babu ranar dainawa.”

Sai dai kuma a raddin da Kakakin Watsa. Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, Buhari ya ce bai ji dadin kalaman Ortom ba.

Ya ce a matsayin sa na shugaban kasa, kowa na sa ne a kasar nan. Kuma ba ya jin dadin kashe-kashe da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a fadin kasar nan.

Ya you kira ga gwamnatocin jihohi da sauran al’umma a rika hada kai da jami’an tsaro.

Yayin da Buhari ke shan alwashin cewa gwamnatin sa ta kusa shawo kan matsalar tsaro, ya kuma yi kira ga dukkan kabilu da mabambanta addinai su ci gaba da zaman lafiya da juna.

Share.

game da Author