Harin ‘Boko Haram’ ya haddasa sallamar ma’aikata 56,000 a Mozambique lokaci guda

0

Kamfanin mai na TOTAL ya dakatar da dukkan ayyukan gina tashar gas da ya ke yi a kasar Mozambique sanadiyyar harin da kungiyar Ansarul Sunna masu kokarin tilasta aiwatar da shari’ar Musulunci a kasar su ka kai masu.

TOTAL ya bada sanarwar janye dukkan ma’aikatan sa kusan 1,000 kuma ya tsaida aikin dungurugum saboda hare-haren da mayakan ‘Ansarul Sunna’ ke yawan kaiwa a yankin Cabo Delgado.

A ranar Litinin din nan bayan tsaida aikin da TOTAL ya yi sanarwa, Shugaban Kungiyar Masu Hada-hadar Cinikayya na Mozambique, Agustina Vuma, ya bayyana cewa idan aka tsaida aikin, kasar za ta yi asarar sama da dalar Amurka milyan 90.

Ana gudanar da gagarimin aikin samar da tashoshin gas a Mozambique, aikin da masana tattalin arzikin kasar ke kallon zai farfado da tattalin arzikin kasar.

Tsaida aikin da TOTAL ya yi zai kuma shafi kananan kafanoni kimanin 410, kama daga masu yin aikin tsaro, leburori da kamfanonin kai kayan aiki daban-daban a masana’antar.

TOTAL ya ce ya tsaida aiki har sai yadda hali ya yi sakamakon rashin tsaro da tashe-tashen hankulan masu tsatstsauran ra’ayin addini a yankin.

Ko a cikin watan Maris sai da Ansarul Sunna su ka kai hari a garin Palma, babban gari da ke yankin Cabo Delgado.

TOTAL na gudanar da aiki na kimanin dala biliyan 20 a yankin Cabo Delgado.

Dama kuma Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya yi gargadin yunwa ta kusa barkewa a yankunan da Ansarul Islam su ka hana zaman lafiya a Mozambique.

Su Wane Ansarul Sunna?:

Ansarul Sunna wasu matasa ne masu akidar kafa shari’ar Musulunci a tilas a kasar Mozambique.

Sun kafa kungiyar cikin 2012 a karkashin akidar Salafiyyah, irin wadda Boko Haram ta kafu a Najeriya.

Akidar Ansarul Sunna iri daya da ce da ta ISIS (Islamic States of Iraq and Syria) da kuma ISISL (Islamic State of Iraq, Syria and Levante).

Haka kuma irin akida daya ce da ta ISWAP (Islamic State of West Africa.

Share.

game da Author