Idan ba a manta ba, fitacciyar ‘ya gwagwarmaya da ta yi ce a shafukan sada zumunta wajen yaki da wasu manufofin gwamnati, ta bayyana cewa sai inda karfin ta ya kare wajen ganin ministan Sadarwa Isah Pantami ya sauka daga kujerar minista a Najeriya.
A wani Bidiyo da ta fitar kuma ya karade shafukan yanar gizo, Aisha Yesufu ta bayyana cewa, tan goyon bayan masu kira ga Pantami ya sauka daga kujerar sa na minista saboda zargin alaka da ya ke da shi da ta’addanci, wanda ya tabbata ba haka bane.
Da kan sa Pantami ya bayyana cewa babu alaka da yake da shi da kungiyar Boko Haram ko kuma Al-Qaeda da Taliban.
Sai dai ‘yar gwagwarmayar ta ce sam bata amince da kalaman pantami ba, matsayarta shine dole ya sauka daga kujerar minista, kuma zata jagoranci gagarimin zanga-zanga da ba’a taba yi a kasar nan ba don ganin ta cimma burinta.
Yan Najeriya da dama, sun tofa albarkacin bakunan su game da wannan abu, inda suka yi tir da hayayyakewar da Aishar ta ke yi game da abinda ba haka bane.
Da ya wa sun tuna sar da mutane cewa, tana daga cikin mutanen da suka goyi bayan zanga-zangar EndSars wanda bata haifar wa Najeriya da alkahiri ba, in banda asarar dukiyoyi da rai da aka yi.
Masu karatu sun bayyana cewa lallai wannan zargi da ake yi wa Pantami, bita da kulle ake yi masa saboda ya yi abinda ba a taba yi ba a ma’aikatar sadarwar Najeriya.