Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya fito a karon farko tun bayan saukar sa daga mulki, ya yi wa Shugaba Joe Biden kaca-kaca.
Trump wanda a cikin rafafan kalaman da ya yi wa Biden, ya nuna cewa ba a taba yin gwamnatin da watanni biyar din farkon kafuwar ma jafa’i da bala’i ba ne a tarihin Amurka, kamar gwamnatin Biden.
A cikin kalaman Trump, ya yi nuni da cewa zai sake tsayawa takara zaben shugaban kasar Amurka a 2024.
“Kowa ya ga irin gagarimar rawar da na taka a watan farkon hawa na shugabancin Amurka. Na jaddada kuma na karfafa tsantsar kishin Amurka, yanzu kuwa mun koma hannun ’yan babu ruwan mu da kishin Amurka.”
Haka Trump ya shaida wa dimbin magoya bayan sa a babban dakin taron wani kantamemen otal da birnin Orlando da ke Jihar Florida.
“Zan iya sake tsayawa takara, ko don na kara karfafa jam’iyyar mu ta Republican, mu sake kama kujerar shugabanci kuma kwace karfin Majalisar Amurka cikin 2022 a lokacin zaben kakar rabin wa’adin Shugaban Kasa.
A jawabin da Trump ya shafe mintina 90 ya na magana, ya nuna babu wani dan takarar shugabancin kasa a bangaren Repubican sai shi har zuwa yanzu.
Ya kara da cewa irin yadda jama’a su ka nuna gamsuwa da irin salon mulkin sa hakan na nufin shi kadai ne zai iya sake dambarwar kokawa da Biden ya kayar da shi.
Har yau Trump na nan kan bakan sa cewa magudi da murdiyya da fashin kuri’u aka yi masa.
Sai dai kuma ya nuna damuwa da mamakin yadda manyan alkalai uku na Kotun Koli, wadanda biyu dga cikin su ma shi ne ya nada su, amma har ba su da karfin halin da za su maida kai a saurarin zargin magudi da Trump ya yi.
A duk lokacin da Trump ya ji wani kalamin da ya zaburar da magoya bayan sa a wurin taron, sai ’yan jagaliyar sa su rika kambama shi da kirari: “Kai ne ka lashe zabe. Kai ne ka yi nasara.”
‘Sai mun kakkabe mugayen iri a Majalisar Amurka’ -Trump
A cikin jawabin na sa, Trump ya bayyana sunayen wasu ‘yan majalisa kuma ‘yan jam’iyyar Republican su goma da su ka amince a tsige shi, mako daya kafin saukar sa. ya kuma fadi sanatoci shida wadanda su ka amince a gurfanar da Trump kotu bayan saurkar sa.
Trump ya ce dukkan ‘yan majalisar da su ka nemi a tsige shi ko a gurfanar da shi, duk ‘yan gangan ne, ma’abota bin kwararo-kwararon Birnin Washington sun a jagaliyanci.
Sai dai kuma Fadar White House ta maida wa Trump raddin irin bulkara da barababiyar da ya rika yi a Fadar White House alhali ya na shugaban Amurka, abin da su ka ce ya zubar wa mukamin sa, fadar da kuma Amurka da Amurkawa mutunci a idon duniya.