SATAR DALIBAN KAGARA: Gwamnan Neja da Sanata Shehu Sani sun watsa wa juna kasa a Ido

0

Gwamna Abubakar Sani Bello da tsohon Sanata Shehu Sani sun tofa wa juna kakin majina sanadiyyar lalacewar Sakandaren Kimiyya ta Kagara, inda a can ne masu garkuwa su ka yi awon gaba dalibai da kuma wasu iyalan malaman makarantar.

Sanata Shehu Sani dai ya nuna matukar damuwar sa da yadda aka yi tattaki har cikin makarantar aka saci mutum 38. Sannan kuma ya nuna takaicin yadda gwamnatin jihar Neja ta bar gine-ginen makarantar a lalace babu gyara.

Sanata Sani ya kara zakalkalewa ya na nuna damuwar sa saboda shi tsohon dalibin makarantar ne. A can ne ya yi makarantar sakandare ta Kagara.

Daga cikin wani sakon Twitter da Sanata Shehu Sani ya fitar a ranar Lahadi, ya yi roko ga Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja, inda ya nuna masa cewa ya rage ciki, ya waiwayi Kwalejin Kimiyya ta Kagara, ya ceto gine-ginen ta wadanda su ka koma kangaye.

Sannan kuma Sanata Sani ya nemi gwamnan ya rada wa daya daga cikin dakunan kwanan makarantar da zai gyara sunan Benjamin Habilah, dalibin da masu garkuwa su ka kashe, kafin su tafi da sauran.

Sai dai kuma wannan magana ta Shehu Sani ba ta yi wa Gwamna Bello na Neja dadi ba.

“Zuwa ga @abusbello da @GovNiger, ya kamata ka sake gina Government Science College Kagara sannan ka sake rada wa makarantar sunan dalibin da ’yan bindiga su ka kashe a lokacin da su ka dira makarantar.”

Sai dai kuma maimakon Gwamna Bello ya karbi shawara ko ya ki karba daga Shehu Sani, shi ma sai ya shiga shafin sa na twitter ya maida masa amsa cewa, me ya hana shi ma Shehu Sani ya yi irin haka a mazabar sa, a lokacin da ya ke majalisar dattawa?

Shi ma Shehu Sani ya sake garzayawa cikin shafin san a Twitter, ya rattaba sunayen ayyukan inganta rayuwar al’ummar da ya ce ya samar a lokacin da ya ke sanata.

PREMIUM TIMES dai ta zagaya dukkan gine-ginen makarantar, kuma ta ga yadda su ka lalace.

Wakilin mu ya shiga har dakunan kwanan dalibai masu suna Lafene da Barde, inda a can ne akwa kwashe daliban, aka yi garkuwa da su.

Sanata Shehu Sani dai ya kwatanta lalacewar gine-ginen ajujuwa da dakunan kwanan makarantar tamkar tsoffin gine-ginen tsoffin daulolin Girkawa da na Romawa.

Tun a farkon hawan Gwamna Sani Bello cikin 2015 ya yi alkawarin zai gyara makarantar, amma har aka sake zaben sa karo na biyu ikin 2019 zuwa yau, ba a gyara ta ba.

Share.

game da Author