Sakamakon wani bincike da aka gudanar kan ingancin maganin rigakafin cutar zazzabin shawara ya nuna cewa kashi daya bisa biyar na maganin na da inganci dai-dai da yawan ruwan maganin da ya kamata a yi wa mutum allura da shi.
Binciken ya nuna cewa za a iya amfani da Kashi daya bisa biyar na maganin wajen warkar da zazzabin shawara a jikin mutane da dama a maimakon da yawa da ake bayarwa.
Kungiyar likitocin jinkai MSF ne suka gudanar da wannan binciken.
Kungiyar ta ce bisa ga wannan sakamako gwamnati za ta iya yi wa mutane da dama allurar rigakafi cutar musamman a lokutan da ake fama da karancin maganin rigakafin.
Zazzabin shawara
Jami’an lafiya sun ce idan sauron dake dauke da kwayoyin cutar ya ciji mutum ne ake kamuwa da cutar.
Cutar na iya yin ajalin mutum idan har ba a yi gaggawar zuwa asibiti ba.
Alamun cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, canza nau’in kalan fada ko kwayar Ido zuwa ruwan kwai, Suma da dai sauran su.
Ga hanyoyi 7 da mutum zai kare kansa daga kamuwa da zazzabin shawara.
1. A yawaita amfani da gidan sauro idan za a kwanta.
2. Tsaftace muhalli musamman nome ciyawa a harabar gida da rufe ruwan da ake tarawa domin hana sauro.
3. A saka raga a taguna da kofofin gida domin hana sauro shigowa gida.
4. A fesa maganin sauro domin kashe sauro da kwari.
5. A tabbatar an yi wa yara allurar rigakafin cutar sannan manya za su iya zuwa asibitin gwamnati domin yin allurar rigakafin cutar kyauta idan ba su yi ba.
6. Ma’aikatan kiwon lafiya su zage damtse wajen yi wa duk mara lafiya gwajin cutar.
7. Ya Zama dole ma’aikacin kiwon lafiya ya Kare kansa yayin da yake kula da Madi fama da cutar