Najeriya ta kwace kadarar naira bilyan 183 na Bankin First Bank saboda bashi

0

Wata tsohuwar kakudubar shari’ar da ta ki cin ta ki cinyewa ta harzuka Najeriya kwace naira bilyan 183 daga bankin First Bank, sakamakon kasa biyan diyyar da kamfanin hakar mai na Royal Dutch Shell Limited ya yi ga al’ummar Ejama Ebubu, cikin Jihar Rivers, tun a shekarar 1970.

Cikin wata sanarwa da jami’an ƴan sanda su ka dira da ita a reshen First Bank na Fatakwal, ta na ɗauke da umarnin kwace kuɗaɗen a ranar Talata.

Bankin da kan sa ya fitar da sanarwar tabbatar da lamarin.

Bankin ya ce rikicin wanda ya haifar da gwamnatin Najeriya ta kwace kadarorin ta din, bai yi wa bankin adalci ko kadan ba.

“Wannan rashin adalci ne, haramci ne, rashin mutunci ne kuma karfa-karfa ce aka yi amfani da karfin gwamnati aka yi wa bankin.”

Shi dai Hedikwatar First Bank da ke Lagos ne ya amince zai biya diyyar da aka dora wa kamfanin Shell shekaru masu yawa, kamar yadda wata Babbar Kotun Jihar Ribas ta zartas da hukunci.

To cikin shekarar 2020, sai kotun ta lissafa cewa kudin ruwan diyyar sun rika karuwa ta yadda a shekarar da ta gabata, adadin diyyar ya kai dala miyan 479, kwatankwacin naira bilyan 183.

A cikin 2010 ne dai al’ummar yankin Abubu na jihar ribas su ka kai Shell kara, bisa neman diyyar gurbata masu yanki da kamfanin ya yi a wajen hakar danyen mai.

Jama’ar Ejama Ebubu dai sun rika yin galaba a duk lokacin da Shell ya daukaka kara.

Galaba ta baya bayan nan ta ce wadda su ka a ranar 30 Ga Nuwamba, 2020, inda kotu ta kara jaddada hukuncin da aka yanke tun a cikin 2010.

Asalin rikicin dai ya samo asali ne tun da aka samu tsautsayi a cikin 1970, inda wata rijiyar mai da Shell ke hakowa ta yi tumbudi, har gangunan danyen mai dubbai su ka mallale a cikinteku, wanda hakann ya gurbata yankin Ejama Abubu

ka

“First Bank ba zai biya kudin ba, saboda su ma sun kasa samun yarjejeniyar garanti daga Shell cewa za ta biya kudin.”

Nwosu ya ce Shell bai ce zai biya kudaden ba, saboda malalar da danyen man ya yi ba laifin kamfanin Shell din ba ne, laifin yakin Basasa ne da aka yi ya haifar da malalar danyen man a cikin teku, tsakanin 1967 zuwa 1970.

Malalar danyen man dai ya haifar da kashe kifayen da ke cikin tekun yankin, wadanda su ne abin ci da kuma sana’ar da mutanen yankin su ka dogara da ita.

Nwosu ya ce Shell ba zai taba yarda a kwace masa kadarori haka kawai da rana tsaka ba, domin bankin ya kai kara kan wannan batu shi ma.

Ya ce kamata ya yi a saurari abin da kotun da ya kai karar za ta zartas.

Share.

game da Author