NAJERIYA: Malejin tsadar rayuwa ya cilla sama fiye da tsananin watanni 32 baya – NBS

0

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (National Bureau of Statistics), NBS, ta bayyana cewa a cikin watan Disamba malejin tsadar kayan abinci ya yi gwauron tashin da bai taba yi a tsawon watanni 32 da su ka gabata ba.

NBS ta fito da kididdigar cewa cikin Disamba malejin tsadar kayan abinci ya cilla sama da kashi 15.75, ba kamar watan Nuwamba da ya tsaya 14.89 ba.

An fitar da wannan kididdigar a safiyar Juma’a, wadda a fakaice ke nuna rufe kan iyakokin kasar nan da Gwamnatin Buhari ta yi domin samun sassaucin abinci, bai yi fa’ida ba, sai ma kara samun hauhawar farashin kayan abincin cikin gida da aka rika samu.

Sannan kuma bude kan iyakoki da aka yi cikin makonnin da su ka gabata, har yau budewar ba ta samar da sassaucin kayan abinci a cikin kasa ba.

Yayin da ake cikin wannan halin matsi, gwamnati ta fara shirin sayar da wasu kadarorin ta, domin samun kudaden da za a yi ayyuka cikin kasafin 2021.

Dama kuka a cikin kasafin, saboda rashin kudi gwamnati ta dogara da ciwo bashin naira tiriliyan 5.6 a cikin duniya idan har ta samu.

Cikin makon da ya gabata ne Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa babu kudi kuma babu alamar su domin a diba a yi aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano.

Jama’a sun damu da jin wannan bayani daga bakin Minista Amaechi, daidai lokacin da ake cikin damuwar cewa kwata-kwata babu batun aikin Tashar Wutar Lantarki ta Mambilla a cikin Kasafin 2021.

Cikin watan Afrilu, 2020 ma PRWMIUM TIMES HAUSA ta wallafa cewa Malejin Kuncin Rayuwa ya yi dagawar da bai taba yi cikin watanni 23 ba.

A wancan tsohon rahoton ma, Hukumar Kididdigar Alkaluma ta Kasa (NBS), ta ce farashin kayayyaki, wanda da su ne ake gane kuncin rayuwa ko yalwar arziki, sun nuna cewa kuncin rayuwa a Najeriya ya yi karuwar da bai taba yi ba tsawon watanni 23.

Ya zuwa watan Maris, an jera watanni bakwai a jere duk wata sai farashin kayayyaki sun tashi. Wannan kuwa na da nasaba da rufe kan iyakokin Najeriya da aka yi, sai kuma kulle garuruwa da aka yi a lokacin Coronavirus.

Rahoton Tashin Gwauron Zabon Farashin Kayan Masarufi ya tabbatar cewa an samu tashin farashi zuwa kashi 12.26.

Farashin kayan masarufi da abinci sun rika tashi tun.daga watan Satumba, 2019, bayan an rufe kan iyakokin kasar nan cikin watan Agusta, 2019.

Kulle kan iyakokin ya haifar da karin farashin shinkafa, man girki, abincin gwangwani nau’uka daban-daban da sauran kayan masarufi.

“Garkame Abuja, Lagos da Abuja ya haifar da tsayawar al’amurran aiki, sufurin kayan masarufi da sauran harkokin jigila da aikace-aikace.” Inji NBS.

Cikin watan Maris farashin kayayyaki ya haura da kashi 14.98 cikin watan Maris, a Bauchi, Neja, Bauchi, Kwara, Sokoto Abuja da Jigawa.

Har yau kokarin da Gwamnatin Tarayya ke ta yi don ganin ta rage radadin talauci da kuncin rayuwa a lokacin zaman zulumin kauce wa Coronavirus, bai yi tasiri ba.

Babban dalilin rashin yin tasirin, shi ne korafin da ake yi cewa kudade da kayan tallafin da ake rabawa, ba su isa wajen talakawan da ya kamata a ce su ne suka amfana, ko suka ci moriyar shirin.

Share.

game da Author