KORONA: Daga ranar Juma’a zuwa Litini, mutum 5,407 aka gano kwayar Korona a jikin su a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1244 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –774, FCT-125, Filato-102, Anambra-47, Ondo-46, Rivers-27, Edo-18, Kaduna-16, Ogun-16
Gombe-16, Bauchi-11, Kano-11, Nasarawa-10, Akwa Ibom-7, Sokoto-7, Borno-5, Ekiti-4 da Zamfara-2.

Yanzu mutum 101,331 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 80,491 sun warke, 1,361 sun rasu.

A ranar Lahadi, mutum 1024 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Benue, Zamfara, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 36,875, FCT –13,573, Oyo – 4,323, Edo –3,096, Delta –1,982, Rivers 3,940, Kano –2,455, Ogun–2,700, Kaduna –5,817, Katsina -1,687, Ondo –1,990, Borno –835, Gombe –1,456, Bauchi –1,093, Ebonyi –1,147, Filato – 5,783, Enugu –1,455, Abia – 1,086, Imo –801, Jigawa –419, Kwara –1,495, Bayelsa –569, Nasarawa – 1,101, Osun –1,065 , Sokoto –536, Niger – 477, Akwa Ibom – 519, Benue – 601, Adamawa – 497, Anambra –433, Kebbi –223, Zamfara –159, Yobe – 207, Ekiti –443, Taraba- 226, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Shugaban Kwamitin PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewa gaggawar bude makarantu, Masallatai da Coci-Coci ne suka yi sanadiyyar kara yaduwar Korona a Kasar nan.
Sannan kuma bude filayen jirage sama domin tashi da saukar jiragen matafiya ya taka mahimmiyar rawan wajen kara yada cutar tun a karshen watan Nuwamba 2020.
Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa a kowani mutum shida da za ayi wa gwajin Korona mutum daya ya kamu da cutar a Najeriya.
Wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce rashin kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar da rashin mai da hankali wajen ganin mutane sun kiyaye dokokin na daga cikin dalilan da ya sa cutar ta kara yaduwa a kasar nan.
Kwararrun sun ce yaduwar cutar zai fi haka yawa idan mutane suka ci gaba da bijirewa dokokin gujewa kamuwa da Korona.
Sannan a kwanakin baya gwamnati ta yi gargadin cewa za a samu karuwar yaduwar cutar a watan Janairu domin mutane suna kin kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar a wata Disamba.
A dalilin haka gwamnati umarci a bude duk cibiyoyi da wuraren da ake killace wadanda suka kamu da cutar.

Asibitoci sun fara cika

Zuwa yanzu mutum 100,087 ne Suka kamu, mutum 1358 sun mutu sanann mutun 18,699 na kwance a asibitocin kasar nan.
Gwamnati ta ce akwai yiwuwar za a sake garkame kasa a dalilin yaduwar cutar Korona.

Share.

game da Author