KORONA: Mutum 1,598 suka kamu ranar Asabar a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1598 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –461, FCT-206, Filato-197, Rivers-168, Kaduna-116, Anambra-53, Ogun-49, Ebonyi-47, Edo-42, Sokoto-32, Imo-31, Katsina-31, Oyo-30, Akwa Ibom-27, Delta-16, Kano-16,, Abia-15, Niger-15, Ondo-11, Bayelsa-10, Borno-9, Kebbi-8, Ekiti-7, Jigawa-1.

Yanzu mutum 109,059 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 85,373 sun warke, 1,420 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 22,266 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Juma’a, mutum 1867 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Kaduna, Oyo, Enugu da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –39,723, FCT–14,544, Filato –6,617, Kaduna–6,237, Oyo–4,679, Rivers–4,382, Edo–3,246, Ogun–2,831, Kano–2,577, Delta–2,102, Ondo–2,070, Katsina–1,723, Enugu–1,583, Kwara–1,566, Gombe–1,489, Nasarawa–1,269, Ebonyi–1,206, Osun–1,186, Abia–1,129, Bauchi–1,107, Borno–859, Imo–841, Sokoto – 677, Benue 653, Akwa Ibom–615, Bayelsa 608, Niger–547, Adamawa–540, Anambra–513, Ekiti–466, Jigawa 425, Taraba 258, Kebbi 248, Yobe-207, Cross River–169, Zamfara 162, Kogi–5.

Shugaban kula da ingancin magani da abinci na ƙasa NAFDAC Mojisola Adeyeye ta yi kira ga mutane da su yi hattara domin jabun maganin Korona ya darkako.

“ Har hanzu hukumar NAFDAC ba ta samu sumfurin maganin rigakafin da ak ikirarin an hada ba kuma idan kamfanin dake hada maganin da gaske yake yi ya kawo samfurin maganin rigakafin da yake hadawa domin hukumar ta tabbatar da ingancinsa.

“ Muna kira da yin gargadi ga ‘yan kasuwa kada su fada tarkon wadannan kamfanoni, su fara shigowa da maganin.

Idan ba a manta ba, kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar Korona, ya ce da zaran maganin rigakafin ya iso Najeriya, za a yi wa Buhari da mataimakin sa a talbijin kowa ya gani.

Haka kuma suma gwamnoni, sun yi irin wannan kuri inda suka idan maganin ya iso Najeriya, za su yi allurar a talbijin kowa a jihohin su ya gani.

Hakan wai shine zai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa maganin da gaske ne kuma kmowa ya yarda ayi masa.

Share.

game da Author