Sabuwar cuta ta kashe mutum 15 a jihar Edo

0

Wata cuta da ba a san irin ta ba ta bullo a kauyen Osomegbe-Ekperi dake karamar hukumar Estakor ta tsakiya a jihar Edo, sannan ta yi ajalin mutum 15 cikin kwanaki dan kadan.

Wasu na ganin cutar amai da gudawa ce ta bullo a kauyen amma jami’an lafiya basu tabbatar da hakan ba tukunna.

Cutar ta bayyana ne bayan ambaliyar ruwan da karamar hukumar ta yi fama da shi tun a watan Satumba.

Ibtila’in ambaliyar ya faru a dalilin cikowar ruwan Kogin Neja inda a dalilin haka mutane da dama suka rasa gidaje da gonakinsu.

Sai dai har yanzu gwamnatocin jiha da tarayya ba su ce komai ba akai.

Idan ba a manta ba a shekarar 2020 hukumar NIHSA ta yi gargaddin cewa jihohin dake kusa da Kogin Neja da suka hada da Kebbi, Neja, Kwara, Nasarawa, Kogi, Anambra, Delta, Edo, Rivers da Bayelsa za su yi fama da ambaliyar ruwan sama a watan Satumba.

Mafiyawan lokutta idan aka fitar da sanarwa irin haka kauyuka da dama kan yi watsi da shi har sai an fada cikin halin ha’ulai.

A hira da PREMIUM TIMES ta yi da kakakin hukumar bada again gaggawa ta kasa NEMA Ezekiel Manzo ya ce hukumar ta dauki matakai domin tallafa wa mutanen da ambaliyar ya shafa.

Sannan kwamishinan muhalli Alex Aleije ya ce gwamna Godwin Obaseki ya zai kai dauki ga wadanda suka aikata haka.

Sarkin Onoghie John Musa a hiran da ya yi da PREMIUM TIMES ya ce alkawuran da aka dauka domin kawo wa mutanen da wannan annoba ya fado wa har yanzu ba acika su ba.

Yace har yanzu ana fama da mace- macen mutane a wannan kauye. ” Zuwa yanzu, mutum 15 sun rasu a wannan kauye.

Share.

game da Author