Likitoci 20 sun kamu da Korona a Jihar Kwara

0

Shugaban kungiyar likitoci ARD dake aiki a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin UITH Badmus Habeeb ya bayyana cewa likitoci 20 sun kamu da cutar korona a jihar.

Habeeb ya ce likitocin sun kamu da cutar a wajen aikin kula da wadanda suka kamu da Korona ne a jihar.

“Kamuwa da cutar da wadannan likitoci suka yi ya jefa iyalansu da sauran ma’aikatan asibitocin cikin hadari.

Habeeb ya yi kira ga gwamnati ta wadata ma’aikatan lafiya

Likitoci da dama sun kamu Korona a wajen aikin kula da wadanda suka kamu da Korona.

Babban dalilin da ya sa hakan ke faruwa kuwa shine rashin kayan saka wa na kariya da ma’aikatan.

Share.

game da Author