EBOLA: WHO da sauran kungiyoyin bada tallafi na duniya za su gina dakin adana maganin rigakafin cutar

0

Shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Ghebreyesus ya sanar cewa WHO da sauran kungiyoyin bada tallafi na duniya sun hada karfi da karfe domin gina wajen adana maganin rigakafin cutar Ebola.

WHO ta fitar da wannan sanarwa a shafin ta dake yanar gizo ranar Talata.

Ghebreyesus ya ce gina dakin adana maganin rigakafin zai taimaka wajen samar da maganin dakile yaduwar cutar da sauran cututtuka.

Ya kuma ce za a ajiye magungunan rigakafin cututtukan zazzabin shawara, bakon dauro tare da rigakafin cutar Ebola.

Za a gina dakin ajiyar maganin a kasar Switzerland inda daga kasar za’ a rika daukar maganin rigakafin zuwa kasashen da suka fi bukata.

Kungiyoyin bada tallafi da WHO ta hada hannu da su sun haɗa da UNICEF, kungiyar jinkai (MSF), Red Cross, kungiyar IFRC, Gavi da vaccine Alliance.

Share.

game da Author