Nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa wata mata mai suna Imaan Sulaiman Ibrahim a matsayin Shugabar Hukumar Yaki da Safara da Fataucin Mutane (NAPTIP), ya karya dakar Najeriya wadda aka kafa hukumar a karkashin dokar.
Dokar NAPTIP Ta 2015
Sashe Na 8 (1) na Dokar NAPTIP ta 2015 ya gindiya cewa: Duk wanda za a nada a matsayin Darakta Janar na NAPTIP, to ya kasance ma’aikatacin gwamnati ne, wanda a inda ya ke aiki matsayin sa ya kai daidai da na Darakta Janar. Ko kuma a iya daukowa daga wasu hukumomin tsaro, wadanda aikin su ya jibinci aikin da Hukumar NAPTIP ke yi.”
Amma abin mamaki, takardun karatu da bibiyar inda Imaan ta yi aiki, sun nuna tsakanin ta da NAPTIP, hanyar jirgin daban, ta mota ma daban.
“Zai kasance kuma wanda za a nada din, Shugaban Kasa ne zai nada shi, amma a bisa sharadin cewa Minista ne zai kai sunan sa, shi kuma Shugaba ya amince bayan ya gamsu da cancantar sa.”
To abin ba haka ya ke ba ga Imaan, wadda ba ta taba yin aikin gwamnati ko na wata daya ba. Kuma ‘yar siyasa ce, sannan kuma ‘yar kasuwa ce mai sayar da kayan kwalisa na shafe-shafen zamani.
A ranar Talata da aka ambaci nadin na su Garba Shehu, Kakakin Shugaba Buhari ya ce kafin nadin Imaan, hadimar Tsare-tsaren Sadarwa ce a Ofishin Karamin Ministan Ilmi.
Saboda haka Imaan ta na rike da mukamin siyasa ne kawai, wanda wa’adin ta zai kare a ranar da wa’adin wannan gwamnati ya zo karshe.
A bangaren matakin ilmi, Imaan ta na shi bakin gwargwado. Ta na da Digiri na Farko kan Ilmin Sanin Halayyar Dan Adam da kuma Digiri na Biyu har guda biyu, ciki har ma da na Ilmin Tafiyar da Harkokin Saye da Sayarwa.
Imaan Ibrahim dai haifaffiyar jihar Nasarawa ce.
Kakakin Yada Labarai ta Ministar Agaji da Jinkai, Halima Oyelode ta ki cewa komai ganin NAPPTIP a karkashin Ma’aikatar Agaji da Jinkai ta ke.
Shi ma Umar Gwandu, Kakakin Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya kasa cewa PREMIUM TIMES komai.
Data ita ma Julie Okah-Donli, wadda ta sauka aka nada Imaan, haka ta shekara hudu rike da Hukumar NAPTIP, amma ba ta canccanci mukamin ba, a bisa dokar NAPTIP ta kasa.
Ba a san dalilin cire ta ba, domin sai cikin watan Afrilu 2021 wa’adin ta zai aikin ta zai kare.
Amma kafin nada ta cikin Afril, 2017, lauya ce mai aiki a kamfanin lauyoyi mai zaman kan sa. Ta taba yin aikin lauya a bankin UBA da kuma aikin hadimanci ga Timiprey Silva, lokacin ya na Gwamnan Bayelsa.