Ganduje, gogarman da aka kama ya na danna daloli aljifai, ya karfafa Hukumar Hana Rashawa ta Jihar Kano

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya amince da karfafa sabon Shirin Karfafa Yaki da Cin Hanci da Rashawa daga 2019 zuwa 2023 a Jihar Kano.

Kakakin Yada Labarai na Ganduje, mai suna Abba Anwar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce Ganduje ya sa hannu kan dokar a gaban Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji, kuma hakan ana ganin zai karfafa dakile cin hanci da rashawa a jihar.

“Duk wannan kokarin mu na yi ne domin tattabar da ana gudanar da aiki gaskiya da gaskiya a cikin gwamnati.

“Sannan kuma hukumar nan za ta kara matsa kaimi sosai domin zakulowa da tabbatar da dakile rashawa da cikin aikin gwamnati a Jihar Kano.

“Gwamnatin za ta bai wa wannan hukuma da ke karkashin Muhuyi Magaji Rimin Gado hadin kai. Kuma ba za mu rika yi masa katsalandan ga aikin sa ba.” Inji Ganduje.

Ganduje ya kuma yaba wa hukumar da kungiyoyin yaki da cin rashawa irin su RoLAC da sauran kungiyoyin da ke yaki da cin rashawa, masu ganin an samar da nagartacciyar al’umma ta hanyar kankare cin hanci da rashawa a cikin ta.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin sa ko kadan ba ta yarda da karbar hanci da cin rashawa ba.

A na sa jawabin, Magaji ya ce za a gabatar da daftarin domin jama’a a Ranar Dakile Rashawa ta Duniya, wato 9 Ga Disamba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin fallasar wasu faya-fayen bidiyo da aka rika nuno Ganduje na karbar makudan daloli ya na dannawa aljifan sa a cikin 2018.

Sai dai kuma Ganduje ya kawo cikas wajen binciken na sa da Majalisar Jihar Kano ta yi, inda ya kai kara kotu ta tsaida binciken.

Har yau EFCC ko ICPC ba su binciki Ganduje ba. A karshe ma wannan badakala ba ta hana shi sake cin zabe karo na biyu a jihar ba.

Share.

game da Author