Tsohuwar ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta yi wa Najeriya da kasashen Afrika albishir cewa lallai nan da watanni uku masu zuwa suma za su samun ruwan maganin rigakafin Korona.
Ngozi ta fadi haka ne da take ganawa da ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama a Abuja.
Ta ce zuwa yanzu kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, CEPI, GAVI da sauran kungiyoyin bada tallafi na tattauna yadda kasashen da basu da karfi da kasashe masu tasowa kamar Najeriya za su iya samun maganin rigakafin cutar korona da aka hada cikin gaggawa kuma a farashi mai sauki.
A yanzu dai kamfanin Pfizer da AstraZeneca ne Suka hada maganin rigakafin cutar wanda ke da ingancin kawar da cutar.
Ngozi ta ce ana tattauna yadda za a gaggauta samarwa kasashen da basu da karfi da kasashe maso tasowa samu wannan magani kafin karshen farkon wata hudu na shekara mai zuwa.
Yin haka zai taimaka wa kasashen duniya irin haka samun maganin cikin sauki a maimakon su jira sai kasashen da suka ci gaba sun gama samun maganin.
Bayan haka Ngozi ta ce wasu kasashe 186 sun kafa kungiya kuma sun bude asusu domin tara kudaden da za a tallafawa kasashe masu tasowa 92 a duniya da maganin rigakafin cutar da zarar an hada shi.
Ta ce maganin rigakafin da wannan Kungiya za ta siya za a yi amfani da su wajen yi wa ma’aikatan lafiya, tsofaffi da tsofaffin dake dauke da wasu cututtuka a jikin su sannan da yara kananan allurar rigakafin cutar.
Masana ilmin hada magunguna dake aikin hada maganin rigakafin cutar Korona sun ce nan da karshen 2021 kowa da kowa zai samu maganin rigakafin cutar Korona.
Malaman dake aiki da kamfanin BioNTech da Oxford ne suka fadi haka a taron tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar da UN ta shirya.
Zuwa yanzu kasar UK ita ce ƙasa ta farko a duniya da ta amince da maganin rigakafin korona da kamfanonin Pfizer da BioNTech suka hada.
Gwajin sahihanci da ingancin maganin da hukumar MHRA ta yi ya kai kashi 95.
Tuni wadannan kamfanonin sun fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar da maganin da suka hada a Disemba.
Discussion about this post