RANAR CIWON SIGA: WHO ta kirkiro sabon hanyar dakile kamuwa da ciwon Siga a duniya

0

Kungiyar kiwon lafiya WHO ta kirkiro wani shiri mai taken ‘Global Diabetes Compact’ domin tallafawa kasashen duniya wajen dakile yawan kamuwa da ciwon siga.

Kungiyar ta yi wannan sanarwa ne a taron ranar ciwon siga ta duniya da ake yi duk ranar 14 ga Nuwamba.

Shirin zai hada sa yin amfani da tsoffi da sabbin matakai domin inganta kula da masu fama da ciwon siga

Shirin zai wayar wa mutane kai kan sanin illar kiba a jiki da hanyoyin rage kiba musamman ga matasa domin kare su daga kamuwa da ciwon.

WHO ta ce za ta yi amfani da kungiyoyi masu zaman kansu, kungiyoyin bada tallafi da gwamnati wajen aiwatar da shirin.

PREMIUM TIMES ta buga labarin wani sakamakon binciken WHO da ya nuna cewa kashi 18.3% na mutanen da cutar korona ta kashe a Afrika na fama da ciwon siga wato ‘Dibeties’ a daidai lokacin da suka kamu da cutar.

Binciken ya kuma ya nuna hadarin da masu dauke da ciwon siga ke ciki a wannan lokaci da annobar korona ta dabaibaye duniya musamman ga wadanda ke da shekaru 60 zuwa sama.

Ciwon siga (diabetes) cuta ce dake kama mutum idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu wato Insulin.

Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.
Rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da ciwon siga.

Alamun wannan ciwo sun hada da yawan jin kishi, yunwa, yawan yin fitsari, kasala da dai sauran su.

Share.

game da Author