Rabon da fannin bunkasa hada-hadar noma a bangaren mata ya samu rashin bada muhimmanci, tun cikin 2017, sai fa a kasafin 2021, inda nan ma aka dan yafuta wa fannin ‘yan kudi cikin cokali.
A kasafin 2021, an ware wa bangaren mata naira milyan 416 a fannin aikin gona da kasuwancin kayan gona, duk kuwa da cewa sun fi maza himma da yawa wajen noma abinci mai tarin yawa a kasar nan.
Mata ke bada gudummawa kashi 75 zuwa 85 a samar da abincin da ake nomawa a Najeriya.
An fi sanin mata da kusantaka da kayan abincin da ake fitarwa kasashen ketare. Irin wadannan kayan gonar sun hada da koko, roba, auduga.
Sannan kuma sun dan maida hankali wajen nau’o’in kayan abinci irin su masara, barkono, rogo da alayyahu.
Akwai kuma mata da dama masu kiwon dabbobi, kaji da kifi.
Harkokin noma kayan abincin sayarwa da tsarin hada-hadar cinikiyyar kayan gona duk sun jibinci harkokin noma gadan-gadan a kasafin ayyukan noma a Najeriya.
Kasuwancin kayan gona ya danganci sukkan hada-hadar kayan gona da ake sayarwa son a samu kudi.
A shekarun baya an fara bai wa harkar kasuwancin noma muhimmanci, domin tabbatar da bunkasar noma a Najeriya.
Masana sun ce a lokacin an kamo hanyar bunkasa noma a kokarin gwamnati na bunkasa wasu fannoni, an fara goyayya da bangaren man fetur wajen samun kudin shiga.
Sai dai kuma duk wannan kokari da gudummawa da mata ke bayarwa a fannin hada-hadar kasuwancin noma, ana fuskantar karanci filin noma ko gonaki.
Action Aid Najeriya ta roki gwamnatin a kara kaimi wajen bunkasa mata a fannin noma, musamman idan aka yi duba da yadda cutar korona ta kassara jama’a, kuma ta kassara sana’o’in su.
Kasafin 2017: A kasafin 2017, an ware wa harkokin noma da cinikiyyar kayan noma na mata naira milyan 657.705.
Amma a shekara ta 2018, an kara shi zuwa naira milyan 818.207.
Da shekarar 2019 ta zo, kasafin ya koma naira milyan 749.581. A 2020 sai aka zabtare ya koma naira milyan 468.36.
Amma a kasafin 2021, kasafin na harkokin noma da cinikiyyar kayan noma ga mata ya fadi kasa warwas zuwa naira milyan 416. 59. Rabon da kasafin ya yi karanci shekaru hudu kenan, tun cikin 2017.
Discussion about this post