Nan ba da dadewa ba za bude tashoshin jiragen saman Kano da fatakwal – Gwamnatin Tarayya

0

Darakta-Janar din Hukumar NCAA, Musa Nuhu ya bayyana wa manema labarai ranar Alhamis cewa nan ba da dadewa ba za a bude filayen jiragen saman Kano da na fatakwal.

Nuhu ya ce akwai sauran gyare-gyare da suka rage kadan da za ayi tukunna kafin a bude tashoshin jiragen saman na Kano da na fatakwal din.

” Akwai sauran ayyuka da suka rage da za a yi tukunna wadanda suka hada da samar da na’urori da kayyade yawan mutanen da za su rika zuwa aiki da kuma hidimomi a tashoshin.

Nuhu ya ce ana kokarin ganin an bude tashoshin saboda a rage wa na Abuja da Legas cinkoso da suke fama shi.

Share.

game da Author