Tubabben dan Boko Haram ne ya shirya tuggun kisan Kanar Bako -Sanata Ndume

0

Sanata Ali Ndume daga Jihar Barno, kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, ya ce wani tubabben dan Boko Haram da gwamnati ta yi wa afuwa ne sanadin kisan da aka yi wa Kanar D.C Bako.

Ndume ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya ke hira da manema labarai, jim kadan bayan kammala zaman Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa.

A zaman, mambobin kwamitin sun saurari bayanin kasafin kudin 2021 da aka ware wa Sojojin Najeriya, kudaden da Sanata Ndume ya ce sun yi kadan.

Ya shaida wa manema labarai cewa shirin da Gwamnatin Tarayya da Hukumar Sojojin Najeriya ke yi, su na yafe wa ‘yan Boko Haram tare da koya masu sana’o’i, sannan su maida su cikin jama’a a matsayin tubabbu, aikin baban-giwa ne kawai.

Ndume ya ce ya sha nanatawa bai goyi bayan shirin ba, kuma dukkan mambobin Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dattawa ba su goyon bayan shirin.

“Ta yaya za a rika yafe wa ‘yan ta’addar da ke kashe mutane, ana yi masu shirin kankare masu mummunar akida, a koya masu sana’o’i sannan a maida su gidajen su, alhali ba a gama yaki ba? Wannan ba dabara ba ce. Kuma ba zan taba goyon bayan shirin ba.

“A garin mu Boko Haram sun tattara dattawa masu shekaru sama da 60 har 75, su ka kai su mayanka, su ka yi masu yankan-rago. Kuma sai a yafe wa irin wadannan ana tsakiyar yaki, a maida su cikin jama’a?

“Tubabben dan Boko Haram ne ya rika bai wa abokan ta’addancin sa bayanan duk wani motsi da Kanar Bako ya ke yi, inda ya ke da inda zai nufa. Ta haka su ka galaba su ka kashe shi a Damboa.” Inji Ndume.

Ya ce kudaden da aka ware wa sojoji cikin kasafin 2021 sun yi kadan. Sannan kuma ya bada shawarar a rika gaggawa wajen sakar wa sojoji kudaden da su ke bukata daga cikin kasafin kudin su.

Mutane da dama su na kokawa kan shirin da Gwamnatin Buhari da Hukumar Sojan Najeriya ke yi, inda ake yafe wa dan Boko Haram din da ya mika wuya, ya yi saranda.

Ana tattara su a wata cibiya, ana ba su horon koyon sana’a, nasihohi da wa’azin wanke masu kwakwalwa domin nesanta kan su daga ta’addanci idan sun koma cikin jama’a.

PREMIUM TIMES HAUSA ta sha buga labaran yadda ake kankare masu akidar ta’addanci da kuma yawan wadanda aka yaye a tura gida.

Ko a ranar Labara sai da Kwamitin Kula da Harkokin ‘Yan Sands na Majalisar Tarayya ya yi korafin cewa kasafin naira bilyan 449 da aka ware wa ‘yan sandan Najeriya a 2021, sun yi kadan.

Share.

game da Author