Boko Haram sun sha luguden wuta daga Sojojin Saman Najeriya

0

Hedikwatar rundunar Tsaron Kasa ya bayyana cewa sojojin saman Najeriya Karkashin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ su yi wa Boko Haram luguden wuta daga sama a sansanonin su dake cikin dajin Sambisa, jihar Barno.

Kakakin rundunar, John Enenche ya shaida cewa sojojin Najeriya na cigaba da samun nasara a kan Boko Haram.

” Bayan nazarin wuraren da ake zaton nan ne inda Boko Haram suke boyewa, sannan kuma an samu bayanai masu gamsarwa, dakarun saman Najeriya sun fantsama wadannan wurare inda suka yi ta yi musu luguden wuta babu kakkautawa.

” An kashe Boko haram da dama a wannan hari kuma an dagargaza sansanonin su a cikin dajin Sambisa.

Rundunar ta bada rahoton cewa sojojin saman sun diranwa Njimia da Dure da ke cikin dajin.

A karshe Enenche dakarun Najeriya za su cigaba da dirkakar Boko Haram har sai sun b ayan su nan ba da dadewa.

Share.

game da Author