Ya kamata mu san malaman mu da matsayar su a yau, Daga Umar Musa

0

Malaman addini suna sarayar da darajar su, a duk lokacin da suka zama yan amshin shata. Duk rayukan da ake kashewa ba tare da hakkin shari’ah ba, basu isa hujja ga malaman addini na kowace kungiya su fadawa gwamnati gaskiya ba amma kowanen su a shirye yake yayi amfani da mambarin massalaci ko majalisin daukar karatu ya kare kungiyar shi ko Gwamnatin da take bashi abin batarwa.

Wannan babban abin takaici ne da yake kara bayyana dabi’un son abin duniya, da ita kanta duniyar a idanun wadanda suke da kyakyawan zato a gurin daukacin dukkan malaman kungiyoyin addinin musulunci. Musamman wanda basa iya nuna bacin ransu a fili karara dangane da daukar rayukan alummar da basu ji basu gani ba. Kuma a haka wani mutum da yake ikirarin malantaka zai daura wani akan wata aqida wacce shi kadai zata biyawa bukata ba wai addinin musulunci da musulmai ba.

Akwai bukatar ire-iren wadanan malaman dasu bayyanawa duniya cewa sun zabi duniya da abin cikin ta, akan bin tafarkin Allah da manzon tsira. Domin gaba daya ayyukan su sun sha bambam da koyarwar manzon tsira da sahabansa. Yanzu mutane sun fi jin tsoron talaucin duniya akan mahaliccin su, kowane malami so yake yayi shura ba ta fannin bawa alumma ilimi ba, sai ta fannin mallakar dukiya ko shugabanci.

Kuma a haka malaman da suka mayar da mabiyansu kamfanonin samun kudi ko mukami a cikin gwamnati, suke so a ringa basu girma alhalin sun saudewa koyarwar shugaban halitta. Ya kamata wadannan malamai su farka daga dogon baccin da suke domin duniya ta wuce inda suke zato.

Idan neman duniya ya hana su fadawa shuwagabanni masu rike da madafun iko gaskiya akwai mutanen da basa ikirarin malamta amma Allah ya hore musu ilimi da kawa zucin da zasu bigi kirji su fadawa kowane shugaba gaskiya komai dacin ta. A wannan gabar nake so in tunasar da ire-iren malaman nan da su gane cewa ya zama wajibi agare su da su ajjiye kwadayin abin duniya tare da rungumar fadakarwa da da’awah tsakani da Allah ba don samun abin duniya ba.

Lokaci yayi da irin wadannan malamai daga kowane bangaren kungiyoyin addini zasu kare daraja da baiwar da Allah ya basu a matsayin su na magada annabawa, addinin Allah ba addinin da za a ringa siyan shi da kudi bane domin wasu tsirarun mutane suji dadin rayuwar su ba. Ya zama wajibi dukkan rayuwar malamanmu ta gino akan koyarwar shugaban hallita Alaihi salat wa salaam.

Babu nuna kwadayi ko son rai dangane ga dukkan wata matsalar rayuwa, idan har malaman addini suka gaza fadawa shuwagabanni gaskiya to wane irin mutane ne ya kamata ace sun zama alkibilar alumma a duk lokacin da wata matsalar rayuwa ta bijiro?

Share.

game da Author