KORONA: Mutum 143 suka kamu a Najeriya ranar Juma’a

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 143 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –70, Kaduna-25, FCT-22, Ogun-11, Filato-4, Oyo-4, Ekiti-3, Osun-2, Edo-1 da Kano-1.

Yanzu mutum 65,982 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 61,782 sun warke, 1,163 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,035 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,836, FCT –6,444, Oyo – 3,702, Edo –2,691, Delta –1,823, Rivers 2,942, Kano –1,771, Ogun –2,145, Kaduna –2,839, Katsina -970, Ondo –1,727, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 752, Ebonyi –1,055, Filato -3,737, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 327, Kwara –1,088, Bayelsa – 426, Nasarawa – 485, Osun –944, Sokoto – 165, Niger – 283, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 92, Ekiti – 351, Taraba- 156, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

A ranar 19 ga watan Nuwanba ne PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa mutum sama da 250,000 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar korona a Amurka.

‘Wordometer’ da ke fidda alkaluman bayanan halin da kasashen duniya ke ciki game da annobar ya fitar cewa ana cigaba da samun hau-hawan yawan mutanen dake kamuwa da cutar a kasar da kuma wadanda ke rasuwa a kullum.

A makon da ya gabata akalla mutum 1,167 suka mutu a cikin uni daya.
A yanzu dai Amurka ita ce kan gaba wajen samun yawan mutanen da korona ta kashe a duniya.

Mutum miliyan 11.8 ne suka kamu da cutar a Amurka a yanzu haka.

A yanzu mutum miliyan 56 ne suka kamu da cutar sannan miliyan 1.3 sun mutu a duniya.

Share.

game da Author