Katafaren kamfanin yin taki na Dangote dake Legas zai fara aiki a watan Disemba, kamar yadda mahukuntan kamfanin suka sanar.
Darektan yada labarai na Kamfanin Anthony Chiejina, ya fadi haka da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja.
Wannan katafaren kamfanin shine mafi girma a Nahiyar Afrika.
Dama kuma kasa irin Najeriya musamman na bukatar irin wannan Kamfani ko dan yadda mafi yawa daga cikin mazauna musamman karkara da manyan biranen su dake Arewacin Najeriya da noma suka dogara.