Gwamnati jihar Neja ta musanta labarin da aka yi ta yadawa wai wasu kwamishinonin jihar uku sun kamu cutar korona a jihar.
Sakataren gwamnati kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar korona na jihar Ahmed Matane ya karyata haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Laraba a garin Minna.
Matane ya ce labaran da ake ta yadawa wai wasu kwamishinoni uku sun kamu da cutar korona a jihar, shirgegen karya ne, kuma ya yi kira ga mutane da su daina yada ire-iren wadannan labarai na karya domin gujewa tada hankalin mutane.
Ya tabbatar cewa gwamnati na iya kokarinta wajen ganin ta tadakile yaduwar cutar a jihar.
Matane ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar a jihar domin Kare kansu.
Zuwa yanzu mutum 277 be ke dauke da cutar korona a jihar Niger.
Daga ciki mutum 6 na kwance a wurin killace masu dauke da cutar, mutum 259 sun warke sannan 12 sun mutum.
Mutum 63,173 suka kamu da cutar a Najeriya zuwa yanzu, mutum 59,634 sun warke, 1,151 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,375 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 21,483, FCT –6,165, Oyo – 3,461, Edo –2,669, Delta –1,816, Rivers 2,846, Kano –1,752, Ogun –2,061, Kaduna –2,668, Katsina -953, Ondo –1,687, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 715, Ebonyi –1,049, Filato -3,652, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo –619, Jigawa – 325, Kwara – 1,069, Bayelsa – 413, Nasarawa – 483, Osun –930, Sokoto – 165, Niger – 277 , Akwa Ibom – 295, Benue – 493, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 335.
Taraba- 151, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.