Ka daina balagoron zuwa asibitin kasashen waje, ka rika zuwa asibitin fadar shugaban kasa – Sanata Danjuma La’ah ga Buhari

0

Sanata Danjuma La’ah dake wakiltar Kaduna ta Kudu, a majalisar Dattawa ya gargadi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da ya daina balagoron zuwa kasashen waje a duk lokacin da bashi da lafiya, ya rika zuwa asibitin fadar shugaban kasa.

Sanata La’ah ya yi wannan gargadi ne a wajen sauraren kare kasasfin fadar shugaban Kasa da babban sakaatren fadar ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa.

” Ina ganin babban dalilin da ya sa asibitin fadar shugaban kasa ya ragwargwabe shine kin ziyartar asibitin da shugaban kasa yake yi don a duba shi, sai dai kasashen waje.

” Da yana ziyartar asibitin da shi da wasu manyan jami’an gwamnati da an gyara asibitin da gaggawa.

” Bai kamata a ce da zarar shugaban kasa ya ji baya jin dadi a jikin sa , sai a waske da shi kasashen waje. Kamata yayi sai an duba shi a tukunna a asibitin kasar nan kafin kuma idan ya zama dole a fice dashi sai a fice da shi, amma ba da zarar yace fim sai a dare jirgi sai kasashen waje ba.

” Mun amince da kasafin ku, naira biliyan 1.3. Kuma muna so da zarar kun samu wadannan kudade a hannu ku ku gaggauta gudanar da ayyuka a asibitin. Muma farincikin mu ne ace a lokacin mu an kammala wannan asibiti ta fara aiki 100 bisa 100.

Umar ya ce lallai da zaran an saka hannu a kasafin kudin 2021, zai tabbata an karisa gina asibitin sannan an wadatrar da kayan aiki na zamani domin shugaban kasa da manyan jami’an gwamnati.

Share.

game da Author