Babbar tashar wutar lantarkin Najeriya ta durkushe

0

Babbar tashar raba harken lantarki ta kasa ta fuskanci gaggarimar matsala a ranar Lahadin nan, yayin da ta fara dawurwura, a karshe ma ta durkushe.

Babban Janar Manaja mai kula da fannin yada labarai da hulda da jama’a, na Kamfanin Bada Wuta na Najeriya (TCN), Ndidi Mbah ya bayyana haka ranar Lahadi a Abuja.

Mbah ya ce ya na mai bakin cikin shaida wa ‘yan Najeriya cewa wajen karfe 11:30 na rana Babbar Tashar Raba Lantarki ta Kasa, wato National Grid ta durkushe.

Amma ya ce nan da nan kwararrun injiniyoyin TCN su ka fara gyare-gyare su ka shawo kan matsalar.

“Yanzu kowace jiha an dawo da wuta, in banda yankunan, Calabar Maiduguri, Gombe, Jos, Yola da sauran su.

“Amma yanzu haka ana ta kokarin ganin a can garuruwan ma komai ya dawo daidai.

“Saboda haka mu na bai wa jama’a hakuri, kuma za a yi bincike domin gano takamaimen dalilin wannan durkushewa da babbar tashar ta yi.

“Domin abin da manaki, ganin yadda kusan tsawon watanni kenan komai na tafiya daidai.” Inji Mbah.

Share.

game da Author