Akalla kashi 15% na mutanen da sauro ya cija za su iya kamuwa da Zazzabin Shawara

0

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Enugu Ikechukwu Obi ya bayyana cewa kashi 15 bisa 100 na mutanen da sauro ya cija za su iya kamuwa da zazzabin shawara.

Kwamishina Peter ya fadi haka ne garin Enugu, a wajen yin feshin maganin Sauro da kwari da aka yi a jihar.

Yadda zazzabin shawara ta kashe mutum 76 a jihohi uku a kasan nan

Idan ba a manta ba hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta sanar cewa mutum 76 sun mutu a jihohi uku a kasar nan bayan sun kamu da wata cuta da ake zargin zazzabin shawara ce.

Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu wanda ya bayyana haka ya ce wadannan mutane sun mutun tsakanin ranar 1 zuwa 11 ga Nuwanba 2020 a jihohin Bauchi, Delta da Enugu.

A lissafe dai mutum 74 sun kama da cutar, 35 sun mutu a jihar Delta.

Mutum 70 sun kamu, 33 sun mutu a jihar Enugu.

Sannan 78 sun kamu, 8 sun mutu a jihar Bauchi.

Wurin gwajin hukumar NCDC dake Abuja ta gwada jinin mutum uku daga Delta, daya daga Enugu sannan takwas daga Bauchi kuma sakamakon ya nuna cewa suna dauke da zazzabin shawara.

Cutar ta fi kama maza masu shekaru 1 zuwa 55 sannan a kan ga alamun zazzabi,yin amai, bahaya da fitsari tare da jini,yawan gajiya, ciwon kai, ciwon ciki da canza kalan fatar jikinsu zuwa ruwan kwai.

Gwamnati ta aika da jami’an kiwon lafiya

Ihekweazu ya ce gwamnati ta aika da jami’an kiwon lafiya domin gudanar da bincike game da bullowar cutar sannan tsaro hanyoyin dakile yaduwar cutar.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, Cibiyar NPHCDA da sauran ma’aikatan lafiya na cikin dakarun sojoji da za su yaki cutar a wadannan jihohi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta rawaito cewa a watan Oktoba 2020 zazzabin shawara ta bullo a kananan hukumomi 7 dake jihohi hudu a kasar nan.

A lokacin gwamnati ta ce ta aika da jami’an lafiya domin dakile yaduwar cutar.

Zazzabin shawara cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cizon sauron dake dauke da kwayoyin cutar.

Allurar rigakafi ne kadai maganin cutar sannan gwamnati ta zuba magungunan rigakafin a duk asibitocin ta domin a rika yi wa mutane allurar kyauta.

Sannan gwamnati ta saka yin allurar rigakafin cutar a cikin jerin allurar rigakafin da ake yi wa yara kanana a domin kare su daga cutar.
Sai dai cutar ta ci gaba da yaduwa a dalilin rashin yin allurar rigakafi da mutane ke kin yi.

Ga hanyoyi 7 da mutum zai kare kansa daga kamuwa da zazzabin shawara.

1. A yawaita amfani da gidan sauro idan za a kwanta.
2. Tsaftace muhalli musamman nome ciyawa a harabar gida da rufe ruwan da ake tarawa domin hana sauro.
3. A saka raga a taguna da kofofin gida domin hana sauro shigowa gida.
4. A fesa maganin sauro domin kashe sauro da kwari.
5. A tabbatar an yi wa yara allurar rigakafin cutar sannan manya za su iya zuwa asibitin gwamnati domin yin allurar rigakafin cutar kyauta idan ba su yi ba.
6. Ma’aikatan kiwon lafiya su zage damtse wajen yi wa duk mara lafiya gwajin cutar.
7. Ya Zama dole ma’aikacin kiwon lafiya ya Kare kansa yayin da yake kula da Madi fama da cutar

Share.

game da Author