ZABEN ONDO: Yadda sojojin ruwa su ka ceto jami’an zabe, bayan jirgin ruwa ya kife da su -INEC

0

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa babu wani jami’in zaben da ya salwanta ko ya samu rauni a hatsarin da jirgin ruwan da su ke ciki ya yi.

Haka kuma INEC ta ce babu wani ko wasu kayan zabe da su ka salwanta a lokacin.

Da ya ke amsa tambayar wakilin PREMIUM TIMES, Babban Jami’in Yada Labarai na Kasa Festus Okoye, ya bayyana yadda sojojin ruwa wadanda ke wa jirgin da jami’an ke ciki rakiya su ka ceto a cikin ruwan.

“Sun tashi daga Igbokada ne zai tafi Karamar Hukumar Ilaje dauke da jami’an zabe da kayaj zabe.

“Ya tintsire a ruwa, amma sojojin ruwa da ke tare da su a wani jirgin sun gaggauta tsamo su, ba tare da asarar rai ko rauni ba.”

Okoye ya kara da cewa kuma ba a yi asarar kayan aiki ko daya ba.

“Lafiya kalau aka tsamo su, kuma sun karasa a daren har ofishin zaben Ilaje. Lamarin ya faru wajen karfe 7 na dare ne a ranar Juma’a.” Inji Okoye.

Share.

game da Author