Jami’an zaɓe da masu jefa ƙuri’a sun dafe keya sun fice a guje, yayin da wani dan jagaliyar siyasa ya dankara harbi a Mazaba ta 4, Rumfar Zaɓe ta 11 a unguwar Ijapo, cikin Akure, babban birnin jihar Ondo.
Lamarin ya faru lokacin da ake kan zabe a rumfar zaben.
Yayin da har yanzu ba a tantance dan jagaliyar ko dan wace jam’iyya ba ne, ‘yan sanda sun ce ba a kashe ko mutum daya da harbin ba.
Wannan ya nuna ‘yan sanda sun karyata ji-ta-ji-tar cewa an bindige mutum daya har lahira.
Kakakin yada labarai na ‘yan sandan jihar Ondo, Tee Leo-Ikoro ya ce wa wakilan mu ba a kashe kowa ba.
“Ba a kai ga gane wanda ya yi harbin ba. Amma bai kashe kowa ba. Haka ma kayan aikin zabe na nan lafiya, ba a lalata komai ba, kuma babu wanda ya salwanta.” Inji Ikoro.