Na yi nadamar yaduwar wasu daga cikin hotunan aure na a shafukan yanar gizo, kuskure ne da ba za a kara ba – Fatima Ribadu

0

Diyar tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, Fatima Ribadu ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda aka rika yada wasu hotunanta da aka dauka a lokacin bikin auren ta a cikin gidan su a Abuja.

Idan ba a manta an daura auren Fatima Ribadu da Aliyu Atiku Abubakar ranar Asabar din da ta gabata a Abuja.

A lokacin wannan taron buki an rika daukar hotuna tare da abokan arziki da yan’uwa da suka halarci bikin.

Wasu daga cikin hotunan da aka rika yadawa musamman a kafafen sada zumunta a yanar gizo da ke nuna kamar rabin jikin Fatima a waje bata ji dadin su ba.

” Na yi aure ranar Asabar 3 ga Oktoba.Akwai wasu hotuna da aka dauka a lokacin bikin a cikin gidan mu wanda a gaskiya banji dadin yada su a yanar gizo da aka yi ba. Na yi nadamar daukar wadannan hotuna kuma ina rokon wadanda basu ji dadin cin karo da wadannan hotuna da suka yi ba su yi hakuri.

” Ina neman afuwan abokaina da iyaye na bisa aikata wannan kuskuren, sannan ina godewa wadanda suka rika kare ni a yanar gizo a lokacin da wasu ke nuna fushin su kan hotunan.

” Sannan kuma akwai rigar da ake sakawa jiki kafin a saka kaya da ya nuna kamar jiki na ne a waje karara, ba jiki na bane yadda kayan suke ne. Ba zan taba yin haka ba. Amma duk da haka na dauki alhakin saka iyaye na, yan’uwa da abokan arziki cikin damuwar yaduwar wadannan hotuna, hakan ya zama min darasi ko dan gaba.

Share.

game da Author